Connect with us

RIGAR 'YANCI

An Nemi Gwamnatin Kano Ta Tallafa Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

Published

on

An yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta tarayya da su tallafa wa al’ummar da ambaliya ya shafa a Kano don rage masu halin radadin da suke ciki. Shugaban Gidauniyar Aminu Zakari Hanga ne ya yi wannan kira a wata zantawa da ya yi da wakilinmu a Kano cikin makon nan.

Alhaji Aminu Zakari Hanga ya ce, yawancin gidajen da ambaliyar ta shafa na marasa karfi ne, don haka akwai bukatar gwamnatin Kano da ta tarayya su tallafa wa farfado da muhallansu da kuma samar musu da kayan abinci cikin gaggawa.
Daga nan sai Alhaji Aminu ya yaba wa Gwamna Ganduje a bisa kafa kwamiti da ya yi da zai bibiyi barnar da ambaliyar ta yi domin duba yadda za a tallafa wa wadanda ambaliyar ta shafa.
Shugaban na gidauniyar Aminu Zakari Hanga ya jajanta wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa, tare da yin addu’ar neman kariyar Ubangiji daga sake aukuwar hakan a nan gaba.
Ya ce, damina ta shigo bana a cikin wani irin yanayi mai dauke da iska mai karfi, wanda ta yaye wa mutane da mafi yawansu talakawa ne gidaje. Don haka suna kira ga Hukumomi da masu hali su taimaka musu don gyara gidajensu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: