An yi kira ga gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari da ta samar wa da kungiyar masu sayar da kayan marmari filinsu na dindindin a garin Funtuwa dake jihar Katsina.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na jihar Katsina Alhaji Yakubu Abdullahi Mai Lemo a lokacin da ya ke hira da manema labarai a ofishin kungiyar da suke haya a Funtuwa.
Alhaji Yakubu ya ce, kiran ya zama wajibi ganin yadda gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari ke kaunar ‘yan kasuwa kuma da son taimakon al’ummar jihar baki daya shiyasa ya yi wannan kira inji shi, sannan ya cigaba da cewar suna da mambobi da yawa a ko ina cikin jihar Katsina babu wani kauye da zaka je baka samu masu saida lemo da ayaba ba ko kankana, ya ce wannan sana’a tasu ta bayar da gagarumin gudun mawar hana zaman banza ga matasan jihar, yanzu akwai sama da matasa dubu 10 masu yin wannan sana’ar akwai masu tura baro suna nan suna gudanar da da wannan sana’a layi layi ga masu kasuwa a tebura, shugaban ya ce a kullum a kalla sai motocin lemo ko na kankana ko ta ayaba sama da 15 sun shigo Funtuwa inda suke gudanar da sana’ar su inda wani bawan Allah ya basu aron fili inda suke tara kayan kafin kananan yan kasuwa su zo su saya su cigaba da saida ma jama’a, sannan ya kara kira ga gwamna Alhaji Aminu Bello Masari da ya taimaki ‘ya’yan kungiyar da bashi domin kananan ‘yan kasuwar su habaka jalinsu, daganan ya kara mika godiyar shi ga gwamnan jihar Katsina a bisa kokarinshi na gina sabuwar tashar mota ta zamani hade da babbar kasuwa ta zamani da sauran aikace aikace da ake gudanarwa a halin yanzu a Funtuwa banda gyaran babbar asibitin garin Funtuwa da manyan magudanun ruwa a fadin garin Funtuwa na bilyoyin Naira da aka yi, ga hanyoyi da fitila masu amfani da hasken rana da Dan majalisa Alhaji Mukhtar Dandutse ya kawo a kananan hukumomin Funtuwa da Dandume da taimakon matasan yankin wajen noman shinkafa da masara da dai sauran abubuwan more rayuwa da aka kawo a yankin ya ce lalle wannan ya nuna basuyi zaben tumun dare ba.
Daga karshe ya yi kira ga dukkan shuwagabannin kungiyar na kananan hukumomi 34 dake jihar su cigaba da biyayya ga wannan gwamnati mai ci yanzu su cigaba da bin doka da oda da biyan kudin haraji don ciyar da jihar gaba da kasa baki daya kuma su cigaba da gudanar da addu’oi na musamman don samun zaman lafiya. Daga karshe ya mika alhinin su bisa gagarumin rashi da aka yi na mamallakin kamfanin jaridar Leadership wanda ya rasu a makon da ya wuce ya ce wannan ba karamin asara aka yi ba na dan kasa na gari wanda ya bada gudunmawa ga jama’ar kasar nan musamman wajen sanin inda kasa ta nufa da sauran aikace aikacen kasar.