Muhammad Awwal Umar" />

An Nemi Magoya Bayan APC Da Suka Hada Kai Dan Ciyar Da Jam’iyyar Gaba

Jam’iyyar APC jam’iyya ce da ta zo da muradun inganta rayuwar al’umma da ciyar da kasa gaba, domin babu jam’iyyar da ta baiwa talaka damar da zai san ana damawa da shi a cikin gwamnati. Dan takarar shugabancin karamar hukumar Chanchanga a jihar Neja, Honorable Zakari Muhammad Kuchi ne ya yi kiran jin kadan da kammala rantsar da shugabannin majalisun dokokin kasar nan.

Hon. Zakari yace ya zama wajibi ga kowani dan jam’iyya wanda ya tsaya takara ya kai labari da ma wanda bai samu nasara, da su san cewar mukami a siyasa ba ne kwarewa da cigaban kasa ba, duk dan jam’iyya na gari ya yi amannar cewar gudunmawarsa ga cigaban jam’iyya shi ne zai iya baiwa jam’iyyar damar sauke muradunta ga cigaban kasa, sanin kowane kasancewar shugaban kasa Muhammadu Buhari akan karagar mulkin kasar nan duk da ‘yan matsalolin da aka fuskanta a baya ya taka rawar ganin wajen ceto tattalin arzikin kasar nan daga dogon sumar da tayi wanda hadin kan da ya samu da kuna irin kyawawan tsare-tsaren jam’iyyar ya ba shi damar samun gamsuwa da amincewar ‘yan Najeriya wajen sake samun zango na biyu akan karagar mulki.

Ina kira ga ‘yan uwana ‘yan siyasa da suka tsaya takara a mukamai daban-daban ba su samu damar haye wa ba, da su tuna gaba na da yawa, kuma hakurinsu ga rashin nasarar su ba kasawa ba ne, illa abinda ake bukata a matsayin su na kasancewar su ‘yayan jam’iyya na gari da su cigaba da marawa muradun jam’iyya da na gwamnati dan ganin an kai kasar ga tudun natsira, kasar nan na neman gudunmawar mu gaba daya, kowa kuma na da rawar takawa wajen ganin cikar wannan nufin, tabbas akwai dubban matasa da ke zaune ba aiki a bayanin maigirma shugaban kasa ya tabbatar da cewar nan da dan wani lokaci dubban matasa ne zasu samu aikin yi a kasar nan, kan gwamnati za ta yi duk mai yiwu wa wajen ganin ta cimma wannan burin na ta.

A jihar nan mun ga irin salon tafiyar maigirma gwamna, mun san inda aka fito kuma kowa ya ga irin gyare-gyaren da ake yi na kawo sauyin da ya sabawa inda aka fito, saboda haka ina yabawa jama’ar jihar nan irin rawar ganin da su ke takawa na baiwa gwamnatin jiha goyon baya ta yadda irin wannan goyon bayan ne yasa gwamnatin jiha ke samun nasarar da ake gani a yau, wanda da nufin Allah idan ya sake tafiya a wasu zangon shekaru hudu kowa zai yaba da irin salon tafiyar.

Hon. Zakari yace zaben Malam Muhammadu Bima Enagi a matsayin sanata mai wakiltar Neja ta kudu babban nasara ce domin ya dade da muradun ganin ya hada kai da gwamnati wajen ciyar da matasan yankin da jihar gaba, sanin kowa ne aikin madatsan ruwa na Baro wani muhimmin abu ne da zai iya samar wa dubban matasa aiki a yankin nan.

Abinda gwamnati ke muradi shi ne samar da ingantaccen wakilcin da zai ahamar da ita akan kyawawan ayyukan da ke gabanta, a wannan karon ina da tabbacin maigirma sanata, Malam Muhammadu Bima da hadin kan gwamnatin jiha lallai za a samar ingantattun ayyukan da zasu cigaba inganta tattalin arziki da cigaban rayuwar jama’a mai anfani. Dan haka ina jawo hankalin sauran bangarorin jihar nan da su cigaba da marawa muradun gwamnatin jiha da na tarayya domin fitar da jihar a sahun gaba.

Exit mobile version