An Nemi Mata Su Cigaba Da Mara Wa Gwamnatin Neja Baya

Daga Muhammad Awwal Umar

An bayyana cewar gwamnatin Neja ta taka rawar ganin wajen inganta rayuwar mata musamman wajen bada tallafi da kirkiro abubuwan da zasu inganta rayuwar mata a jihar, wanda hakan ba karamin cigaba da kulawar da mata su ka samu ba. Kodineta mai kula da hada kan mata a ofishin gwamnan jihar mai kula da yankin Zone B, Hajiya Zarah I. Abdullahi ne tayi yabon kan irin gudunmawar da mata su ka samu a gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello a Neja.

Zarah ta cigaba da cewar a tafiyar siyasa mata mu kan taka rawa sosai kuma duk da cewar majalisar dunkin duniya ta umurci a rika ba mu kaso talatin cikin dari wani lokaci sai ka ga ba a mutunta wannan tsarin, amma bisa jajircewar uwargidan gwamnan jiha, Hajiya Amina Abubakar Sani Bello mun samu duk irin damar da ta dace a wannan gwamnatin, wanda dole mu cewa maigirma gwamna sambarka.

Ko a bangaren ayyukan jinkai kadai bayan dawowarsa karagar mulki karo na biyu ya bullo da shirye shirye da dama sama da dubu daya saboda inganta rayuwar mu kuma mun anfana, ga shirin gwamnati na inganta kiwon lafiya, wanda uwargidan gwamnan Neja ke kulawa da shi musamman a bangaren cutarsa kansa wanda a kyauta a ke kulawa da marasa lafiyar tare da daukar dawainiyar magungunan su da yi masu aiki. Sannan ta himmantu wajen kula da hakkin yara kananan musamman masu yiwa kananan yara fyade da cin zarafin su, wanda a kasar nan idan gwamnatin Neja ba zama ta daya ba to lallai tana sahun gaba wajen mutunta hakkin mata da yara kanana.

Kodinetan ba ta tsaya nan ba, ta cigaba da cewar yanzu haka gwamnatin jiha ta hada kai da kungiyoyi masu zaman kan su wajen horar da mata sana’o’in hannu domin dogaro da kan su dan rage radadin halin da rayuwa ke ciki, bayan tallafin kudade dan yin sana’a da kuma horar da su hanyar samun kudaden shiga yadda ya dace.

Mu mata muna da kyakkyawar alaka da matar gwamna domin itace shugaban mu,domin duk wani abu da ka ga mata sun samu a gwamnatin nan ta dalilinta ne. Wannan ne ya ba ni kwarin guiwa bayan gwamnati ta ba ni wannan damar na samu kai ziyara yankunan kananan hukumomi takwas da ke yankin nan, wanda na saurari bayanai da dama daga gare su na yabo da kulawa wanda su ka bayyana min cewar tun bayan dawowar mulkin dimukuradiyya ba su ga matar da a ka baiwa mukami ta ziyarce su ba sai a wannan karon, ni kuma amannar da na yi da irin salon tafiyar maigirma gwamna shi ya karfafa guiwa na yasa na tashi tsaye dan jin halin da mata ke ciki lungu da sako.

Duk wuraren da na ziyarta a yankunan kananan hukumomin nan, sai na ziyarci matar shugaban karamar hukuma dan in san ayyukan da ta ke yi kuma in san irin bukatun jama’ar nan ga gwamnati, haka iyaye sarakuna ban bar su baya ba, dan in nuna masu gwamnati ta zo da canjin da jama’a ke bukata da neman albarka dukkan su na kusance su kuma ina godiya da irin kalaman da na ke ji game da gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello.

Duka wadannan nasarorin da gwamnati ke samu ya biyo bayan yadda gwamnati ta bar kofarta a bude ga kungiyoyi masu zaman kan su da ke tallafawa jama’a wanda a kowani lokaci su ka bukaci wani tallafi daga gwamnati a ka ba su su kan tabbatar kowani bangare a jihar nan ya anfana.

Ka ga dukkan wannan nasarorin da gwamnatin Neja ke samu ya biyo bayan kwarin guiwar da muke samu ne a wajen ta, a zangon farko na maigirma gwamna mun samu kujerar kwamishina guda biyu, a wannan karon mun samu kujeru guda hudu, kujerar kodineta da mace daya ce amma yanzu mata hudu ne, gaba daya a baya matan da ke rike da kujerar kodineta a bangarori da dama shida ne, yanzu sun kai ashirin. Dan haka maganar baiwa dama matsayi a wannan gwamnatin ba abinda za mu ce sai sambarka, kujerun da mata ke rike da su a gwamnatin nan suna da adadi da dama a kowane bangare na gwamnatin Neja

Abinda na fahimta ba kowane ke son fitowa ya bayyana abinda gwamnati tai masu ba, ni kan zan fito in bayyanawa ‘yan uwana mata musamman wadanda ke yankunan karkara dan su fahimci wadanda ke wakiltarsu a cikin gwamnati, saboda haka ina jawo hankalin ‘yan uwana mata da mu cigaba da goyawa gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello saboda irin damar da ya ke baiwa jinsin mata a cikin gwamnatinsa.

 

Exit mobile version