Daga Mahdi M. Muhammad,
Kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Honarabul Timothy Owoeye ya fadakar da Kiristocin da sauran ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsantsan game da yaduwar cutar korona a karo na biyu.
Ya kara da cewa, a lokacin da muke wannan cutar, mutane da masu ruwa da tsaki a cikin harkar kiwon lafiya suna tsara hanyar mayar da martani da wuri zuwa ga cutar.
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su fara yin taka tsantsan don hana yaduwar cutar daga al’umma yayin da suke bikin tunawa da ranar haihuwar Jisus.
Ya ce, “Ina kuma cajin gwamnatin Jiha da masu ruwa da tsaki a harkar lafiya da su daidaita tsarin tunkarar wuri ga wannan cutar a karo na biyu, domin mun yake ta a karo na farko kuma muna da tabbacin zamu iya yakar ta a karo na biyu. Dole ne mu ci gaba da kuma kunna wani tsarin aiki wanda zai kiyaye mutanenmu a wannan lokacin annobar. Dole ne mutane su tabbatar da cewa duk matakan kariya daga cutar da gwamnatoci ke bada wa sun kiyayewa.”
“Dole ne mu guji yin tafiye-tafiye masu tsayi zuwa ga danginmu, kuma ya kamata a guji saduwa ta zahiri yadda ake yi ada, ya kamata kuma mu yi amfani da fasaha ta hanyar hada kai a yayin bikin Kirsimeti ta hanyar tarho ko taron bidiyo game da saduwa ta zahiri. Nesanta da juna, sanya abin kariya ta baki da hanci a wuraren taron jama’a da kashe kwayoyin cuta a kai a kai yana hana yaduwar cutar,” in ji shi.
Shugaban majalisar ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya masu kyakkyawar niyya da taimakawa marayu a lokacin bukukkuwan karshen shekara, yana mai bayyana cewa, raba kauna da abinci zai taimaka matuka wajen rage tasirin cutar a kan talakawa.