Tawagar ‘yan wasan kasar Ingila za ta fafata da tawagar kasar Poland a rukuni na tara a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2022 a kasar Katar kamar yadda aka raba jadawalin ranar Litinin.
Sauran wadanda ke cikin rukunin sun hada da Hungary da Albania da Andorra da kuma San Marino sannan tawagar Wales za ta kara da Belgium, wadda ta fitar a gasar nahiyar Turai ta Euro 2016, inda za su kara a rukuni na biyar.
Ireland ta Arewa tana rukuni na biyar da ya kunshi kasashen Italy da Switzerland da Bulgaria da kuma Lithuania ita kuma Scotland za ta kece raini da Denmark da Austria da Israel da tsibirin Faroe da kuma Moldoba a rukuni na shida.
Ita kuwa Jamhuriyar Ireland za ta yi gumurzu da Portugal da Serbia da Ludembourg da kuma Azerbaijan sannan za a fara wasannin ne tsakanin watan Maris zuwa Nuwambar shekara ta 2021, sannan a buga wasannin cike gurbi daga Maris din 2022.
Rukuni na uku: Italy da Switzerland da Ireland ta Ireland da Bulgaria da kuma Lithuania.
Rukuni na biyar: Belgium da Wales da Jamhuriyar Czech da Belarus da kuma Estonia.
Rukuni na shida: Denmark da Austria da Scotland da Israel da tsibirin Faroe da kuma Moldoba.
Rukuni na tara: Ingila da Poland da Hungary da Albania da Andorra da kuma San Marino.
Sakamkon yanayi na zafi a Katar, gasar kofin duniya da kasar za ta karbi bakunci za’a fara daga 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga Disambar 2022 saboda hakan zai sa gasar ta zama ta farko da za’a gudanar da ita ba a watan Mayu ko Yuni ko kuma Yuli ba.
Za kuma a gudanar da wasannin a kwanaki 28 da ake sa ran kasashe 32 za su kece raini a filaye takwas a birane biyar da za su karbi bakuncin gasar inda tuni kasar tana ci gaba da shirye shiryen ganin ta samu nasarar gudanar da gasar.
Tawagar kwallon kafa ta Faransa ce ke rike da kofin duniya da ta lashe a kasar Rasha, kuma na biyu da take da shi a tarihi har ila yau ana ganin tana da warfin da zata iya sake lashe kofin a kasar ta Katar.