Abba Ibrahim Wada" />

An Rage Albashin ‘Yan Wasan Firimiyar Ingila Gaba Daya

Kungiyoyin kwallon kafar da ke buga Gasar Firimiya za su bukaci ‘yan wasansu su amince a rage albashinsu da kashi 30 cikin 100 domin gudun korar ma’aikata a daidai lokacin da aka sanar cewa ba za a ci gaba da kakar wasa ta bana ba sai an tabbatar da kiwon lafiya sannan an ga ya dace a ci gaba.

 

Dukkan kungiyoyin sun amince su gabatar da abin da suka kira tsarin rage albashi da kuma jinkirta biyansa ga ‘yan wasansu saboda hakan zai taimakawa kungiyoyin su ci gaba da rike ma’aikatansu.

 

Hukumar Gasar Firimiya za ta mika wa EFL da National League £125m, inda za su hada da nasu £20m su bai wa hukumar kiwon lafiyar Birtaniya domin taimakawa kasar a wajen yakin da takeyi da cutar ta COBID-19. Kungiyoyin sun yi niyyar kammala ragowar wasannin da ake sa ran za su buga, da ma gasar ta Firimiya baki daya domin tabbatar da kungiyar da zata zama zakara a wasannin da ake bugawa a yanzu.

 

An dakatar da EFL, Women’s Super League da kuma Gasar Zakarun Turai ta mata ba tare da bayyana ranar da za a ci gaba ba, hakan na nufin an dakatar da dukkan gasar Ingila sai abin da hali ya yi.

 

An tabbatar ba za a koma buga Gasar Firimiya ba a farkon watan Mayu kuma ba za a ci gaba da kakar wasa ta 2019-20 ba sai an tabbatar da kiwon lafiya da kuma ganin cewa komai ya koma daidai a cewar sanarwar da hukumomin Gasar suka fitar.

Exit mobile version