Connect with us

KASASHEN WAJE

An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Malawi

Published

on

An rantsar da sabon shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera domin waadin mulki na tsawon shekaru 5 a yau Lahadi, yan saoi bayan cire tsohon shugaban kasar Peter Mutharika a zaben da aka sake gudanarwa.

Chakwera mai shekaru 65, ya lashe kashi 58.5 cikin dari na yawan kuriun da aka kada a ranar Talata, wanda ya sauya sakamakon zaben na farko a watan Mayun shekara ta 2019, wanda kuma kotuna suka soke. Masu fashin baki na bayyana sake zaben da aka yi a zaman wani zakaran gwajin dafin karfin da kotuna su ke da shi a Afirka, na magance magudin zabe, da kuma hana shugaban kasa amfani da karfinsa a zaben.

Tare da taimakon ku, za mu dawo da fata a zukatan alumma masu tasowa, na samun gwamnati da za ta yi wa jamaa aiki, ba wai ta mulke su ba, Chakwera ya fada a jawabin da ya yi wa dimbin jamaar da suka tattaru a bikin rantsarwar. Jamiyyar MCP ce ta farkon kafuwa a kasar ta Malawi, kuma nasarar Chakwera ta sake maido da ita kan mulki bayan shekaru 26 na mulkin adawa. Bangaren sharaa na kasar ya rusa sakamakon zaben da aka gudanar a watan Mayun shekara ta 2019 da ya baiwa tsohon shugaba Mutharika waadin mulki na 2 bisa dalilan tafka magudin zabe, kana ta ba da umarnin sake gudanar da zaben.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: