An Rantsar Da Shugaba Buhari A Karo Na Biyu Da Gwamnoni 29

A jiya ne aka rantsar da Shugaba Buhari a karo na biyu a matsayin zababben Shugaban kasar nan, an yi rantsuwar ne a dandalin Eagle Skuare, da ke Abuja.

Mukaddashin Alkalin-alkalan kasar nan, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, ne ya jagoranci rantsarwar da misalin karfe 10:37 na safiyar ranar ta Laraba. Shugaban yana tare ne da Uwargidansa, Aisha, a lokacin rantsarwar.

Tun da farko, mukaddashin Alkalin-alkalan ya rantsar da Mataimakin Shugaban kasa ne, Farfesa Yemi Osinbajo, da misalin karfe 10:25 na safiya. Shi ma yana tare ne Uwargidansa, Dolapo, a lokacin da aka rantsar da shi din.

Bikin rantsarwar ya sami halartan wasu iyalai na kusa da shugabannin.

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Kakakin Majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara sun iso filin rantsarwar ne da misalin karfe 9:40 na safiyan. Bikin rantsarwar ya kuma sami halartar tsaffin shugabannin kasar nan, Janar Yakubu Gowon, da tsohon shugaban gwamnatin rikon kwarya, Cif Ernest Shonekan.

Wakilinmu ya ba mu rahoton cewa, tsaffin shugabannin kasar nan, Olusegun Obasanjo da Ibrahim Badamasi Babangida, ba su sami halartar bikin ba. Sauran manyan bakin da suka halarci bikin rantsarwar sun hada da jakadun kasashen waje da ke nan Nijeriya, shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan, fitaccen dan kasuwan nan Aliko Dangote, Gwamnoni, ‘Yan majalisu, Tsaffin Ministoci, Sarakunan Gargajiya da sauran su.

Hakanan bikin ya sami halartar shugabannin Jam’iyyar APC, da suka hada da shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole, jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Ahmed Tinubu da Cif Bisi Akande, da sauran su.

Wakilinmu ya ba mu labarin cewa, sun ga Saraki da Tinubu suna rungumar juna a wajen bikin. Ya kuma shaida mana an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen filin taron. Manyan abubuwan da za a yi na bukukuwan rantsarwar duk an dage su zuwa ranar 12 ga watan Yuni, sabuwar ranar Dimokuradiyya ta kasar nan.

Akwai kuma sabbin Gwamnoni 12 wadanda wannan ne karon su na farko da hawa kujerar gwamnan da su ma aka rantsar da su din a jiya, sa’ilin da wasu 17 da suka sake komawa bisa kujerun na su, su ma duk an rantsar da su din a ranar ta jiya. Sakamakon zaben da aka yi dai na ranar 9 ga watan Maris, ya nuna cewa, Jam’iyyun APC da ta PDP ne kadai daga cikin jam’iyyu sama da 90 da suka shiga zaben suka sami kujerun gwamna a zaben.

Gwamnonin da suka dare kujerun gwamnan a karo na farko sun hada da, Umaru Fintiri (PDP, Adamawa), Farfesa  Babagana Zulum (APC, Borno), Bala Mohammed (PDP, Bauci), Inuwa Yahaya (APC, Gombe),  Emeka Ihedioha (PDP, Imo), Babajide Sanwo-Olu APC, Lagos), Dapo Abiodun (APC, Ogun), Seyi Makinde (PDP, Oyo), Abdulrazak AbdulRahman (APC, Kwara), Injiniya Abdullahi Sule (APC, Nasarawa), Mai-Mala Buni (APC, Yobe) da Bello Matawalle (PDP, Zamfara). Gwamnonin da suka sake dawowa a karo na biyu sun hada da; Okezie Ikpeazu (PDP, Abia), Dabid Umahi (PDP, Ebonyi), Ifeanyi Ugwuanyi (PDP, Enugu), Udom Emmanuel (PDP, Akwa Ibom),  Ben Ayade (PDP, Kros Riba), Ifeanyi Okowa (PDP, Delta), Nyesom Wike (PDP, Ribers), Samuel Ortom (PDP, Benue), Simon Lalong (APC, Plateau), Abubakar Bello (APC, Neja), Darius Ishaku (PDP, Taraba), Nasir el-Rufai (APC, Kaduna), Abdullahi Umar Ganduje (APC, Kano), Aminu Masari (APC, Katsina), Abubakar Bagudu (APC, Kebbi), Mohammed Badaru Abubakar (APC, Jigawa) and Aminu Tambuwal (PDP, Sakkwato).

A bisa hukuncin da kotun koli ta kasa ta zartar ya nuna Jam’iyyar PDP tana da Jihohi 15 ne, a sa’ilin da jam’iyyar APC ke da Jihohi 14 cikin 29 da aka gudanar da zaben a cikin su. Za a gudanar da zabukan Gwamnonin a Jihar Kogi da Bayelsa ne a watan Nuwamba na wannan shekarar, Jihohin Ondo da Edo a shekarar 2020, Anambra a shekarar 2021, sai kuma Jihohin Osun da Ekiti a shekarar 2022.

Da yawan gwamnoni masu barin gado dai ba su tsaya halartar bukukuwan rantsarwar ba.

Exit mobile version