An Sace Daliban Sakandire 73 A Zamfara

Jami’an ‘yan sanda a jihar Zamfara sun tabbatar da sace daliban makarantar sakandire ta gwamnati a garin Kaya dake jihar ta Zamfara. Rahotanni sun tabbatar cewa da safiyar yau Laraba ‘yan bindiga suka farmaki makarantar dake Karamar Hukumar Maradun.

“Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara na sanar da sace daliba 73 na Makarantar Sakadiren Gwamnati a garin Kaya dake karamar Hukumar Maradun. Gungun ‘yan bindigar sun sace daliban ne da misalin karfe 11 na safiyar yau Laraba.” Inji Jami’in Hulda da Jama’a Na Rundunar ‘Yan Sandan.

Jami’in ya bayyana cewa hukumarsu ta fara aikin hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro don tabbatar da an ceto yaran daga hannun ‘yan bindigar, kuma tuni rundunar tasu ta kai jami’a kewayen garin da abin ya faru.

Exit mobile version