Umar A Hunkuyi" />

An Sake Bankado Wata Cibiyar Gyara Halayyar Matasa A Kaduna

•An ’Yanta Mutane 147 Da Ke Cikinta
A shekaranjiya ne ‘Yan sanda a Kaduna suka kai mamaya wata cibiya da aka ce ana gyara halayyar matasa wacce aka fi kira da Cibiyar Malam Niga, ta gyara halayyar matasa da koya masu sana’o’i, wacce ke anguwar Rigasa, ta karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna, inda kuma ‘yan sandan suka ‘yantar da dalibai 147 da suke a cikin cibiyar.
‘Yan sandan sun durfafi cibiyar ce wacce take a kwanar Gurguwa tun da safiyar ranar ta Asabar inda suka kuma kwashe dukkanin daliban da suke a cikinta zuwa masaukin alhazai da ke anguwar Mando Kaduna.
Wakilinmu ya fahimci cewa, Gwamnan Jihar ta Kaduna, Nasir El- Rufai, ya na cibiyar, ‘yan sandan kuma sun yi awon gaba da wanda ya assasa cibiyar mai suna Lawal Yusuf Muduru, domin yi masa tambayoyi. Wakilin namu wanda ya ziyarci masaukin alhazan da ke Mando inda aka kai daliban cibiyar a karkashin kulawar ma’aikatar kula da jin dadin al’ummar Jihar, ya shaida mana cewa, ‘yan sanda ne suke gadin daliban a masaukin na alhazai a daidai lokacin da jami’an ma’aikatar suke daukan bayanan daliban.
Kwamishiniyar jin dadin al’umma na Jihar, Hafsat Baba, wacce take a masaukin alhazan, ta shaida wa wakilin namu cewa, daliban da aka kwaso din sun kunshi mata 22 sa’ilin kuma da a cikin su akwai ‘yan kasashe makwabtanmu su hudu. “Yawan daliban da aka kwaso daga cibiyar su 147 ne, daga cikin su akwai mata guda 22, sa’ilin kuma da guda hudu sun fito ne daga jamhuriyar Nijar da kuma kasar Kamaru.
Akwai kuma ‘yan kananan yara a cikin su da kuma wadanda su ke da tabin hankali. Mun yi Magana da likitan kwakwalwa wanda mu ke jiran da ya zo domin ya duba su,” in ji ta.
Ta kara da cewa, su na kan daukan bayanan daliban cibiyar da su ka kwaso ne, a kuma daidai lokacin da suke jiran umurni na gaba daga gwamnatin Jihar a kan mataki na gaba. Wakilinmu ya fahimci cewa yawancin daliban cibiyar ‘yan kwaya ne da aka kawo su cibiyar domin a gyara masu halayen su a kuma koya masu sana’o’i kamar sana’ar Kafinta, walda, kwamfuta da makamantan hakan.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da mamayar cibiyar, yana mai cewa, Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai ya kai wata ziyarar bazata a cibiyar tare da ‘yan sandan, inda suka gano cewa ana ajiye da daliban cibiyar ne a cikin halin kunci.
Ya ce, kimanin dalibai mata Bakwai na cibiyar sun yi zargin wasu daliban cibiyar sun yi masu fyade, ana kuma kan duba wannan zargin na su. Ya kara da cewa, wanda ya assasa cibiyar yana hannun ‘yan sanda domin amsa wasu tambayoyi duk da ya na ikirarin ya na da lasisin gudanar da cibiyar.

Exit mobile version