Connect with us

JAKAR MAGORI

An Sake Bankado Wata Haramtacciyar Makarantar Almajiranci

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bankado makarantar da ake tura yara maza da mata almajiranci a Karamar Hukumar Zariya, kamar yadda kwamishinar walwala ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta ce, an samu yara mata 17 masu shekaru daga 8 zuwa 10 a cakude da maza.

Kwamishinar ta ce sun kwashe almajirai 327 daga makarantar Malam Aliyu Maikwari daga cikin 500 din da ya bai wa masauki a gidansa. Gwamnatin jihar Kaduna ce ta damke malamin na tsangaya mai suna Aliyu Maikwari a Karamar Hukumar Zariya.

An zargi malamin ne da cudanya yara maza da mata don almajiranci, majiyarmu ta ruwaito cewa, Gwamnatin jihar ta kwashe almajirai 327 daga cikin 500 da ke gidansa inda ya ba su masauki. Kwamishiniyar walwala ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ce ta bayyana hakan ga manema labarai. Ta ce daga cikin almajiran, akwai 17 duk yara mata ne masu shekaru 8 zuwa 10 kuma an cudanya su ne da sauran kattin almajirai maza a gida daya, ta bayyana cewa wannan ba koyarwar addinin Islama ba ce tare da dora laifin a kan iyayen yara matan da suka kai yaransu.

“A lokacin da aka sanar da ni, ban yarda ba sai da na ga hotunan yaran, kananan yara mata wadanda shekarunsu bai su wuce 10 ba aka hada da yara maza. “Mun kwashe yara 327 daga cikin 500 da ke gidan. Saboda tsaurin idonsa, sai da muka hada da jami’an ‘Operation Yaki’ kafin mu kama shi. “Mun gano cewa yana aurar da kananan yaran da kansa.

A halin yanzu ana bincikarsa a Kaduna,” Ta ce an kama malamin ne a cikin kokarin gwamnatin jihar na mayar da almajirai garuruwansu don hana yaduwar cutar COVID-19. A wani labari na daban, wasu mazauna birnin Kano sun bayyana goyon bayansu a kan dokar hana walwala da shugaban Buhari ya saka wa jihar. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da sanarwar rufe jihar saboda annobar Korona. (NAN)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: