Dan gwagwarmayar siyasar nan kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Mista Omoyele Sowore dai ya fuskaci fushin jami’an tsaro a jajibiren sabuwar shekara inda suka cafke shi a Abuja bisa jagorantar zanga-zangar cikin dare domin kalubalantar gwamnatin tarayya.
Sowore dai shi ne mawallafin kayar hada labarai ta Sahara Reporters, jami’an ‘yan sanda ne suka kama shi bisa jagorantar zanga-zanga a birnin tarayya Abuja bisa kiran samar da rayuwa mai inganci ga ‘yan kasa.
An kira layukan Sowore a safiyar jiya Juma’a amma dukkanin layukansa biyun ba su shiga. Har dai zuwa yanzu ba a samu adadin yawan wadanda aka kama su tare da Sowore din ba.
Har zuwa lokacin hada wannan labarin ba a jiyo komai daga bakin jami’in watsa labarai na ‘yan sanda Mista Frank Mba ba.
Zanga-zangar dai wacce suka fito da ita, da bukatu daban-daban dukka dai da suke nuna rashin gamsuwa da salon mulkin gwamnatin Buhari. Sun fara ne da karfe 11:30 na daren kashegarin sabowar shekara da zimmar za su cigaba da zanga-zangar har zuwa jiya farkon sabuwar shekara.
Sowore ya bukaci masu shiga zanga-zangar da su fito da ababen da za su nuna kiranye-kiranyen da suke da su domin bukatar samar da sauyi da canji.
‘Yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar a yankin Gudu da ke Abuja, inda suka kamu wasu daga cikin masu zanga-zangar.
Wanda har zuwa aiko da labarin nan su na karkashin kulawar ‘yan sandan.
Zanga-zangar mai neman samar da rayuwa mai inganci da kuma neman inganta aikin tsaro tare da sukar gwamnatin Buhari bisa gazawa.
Tunin dai wasu kungiyoyi suka fara kiran a sake Sowore.
Idan za ku iya tunawa dai a farko an taba tsare Mista Sowore na tsawon sama da kwanaki 100 a shekarar 2019 bisa zanga-zangar neman ‘Rabalushin’ da ya yi jagoranta, wanda daga bisa kotu ta bada belinsa.