Umar A Hunkuyi" />

An Sake Kulle Gidajen Mai 11 A Kogi

Sashen kula da albarkatun mai (DPR) a Jihar Kogi ya kulle wasu gidajen siyar da man fetur guda 11 a cikin Jihar.

A cewar shugaban sashen na DPR a Jihar, Amos Jokodola, gidajen man da aka kulle a cikin makon da ya gabata a cikin Jihar sune wadanda ke, Lokoja, Obajana, lsanlu, Okene, Yagba ta Gabas da Yagba ta Yamma, a sabili da saba ka’ida.

Ya bayyana cewa, “Famfunan zuba man na su ba a daidai suke tafiya ba, suna cutar jama’a. kamar kuma yanda doka ta nuna an dakatar da Lasisin gidajen man guda 11. Gidajen man da aka kullen za su ci gaba da zama a kulle ne har sai masu gidajen man sun biya tarar da aka yi masu, sun kuma gabatar da rubutacciyar takardar tuba a kan ba za su kara yin abin da suka yi din ba.

Ya kara da cewa, sashen hukumar na shi a Jihar ya ziyarci gidajen mai guda 53 ne a cikin Jihar a kwanan nan.

Gidajen man da aka kullen sun hada da na, Oduanyo Business Enterprises Inbestment (Egbe), Olubush (Isanlu), Ardor Oil and Gas (Obajana), Ebugrap (Obajana), NNPC Mega 1(Lokoja), Royal Confluence (Lokoja), Always (Okene), Total Plc (Okene), Nice Mohammed Petroleum Company (Lokoja), A.Y.M Shafa (Lokoja) da Sunchy Global Inbestment Resources (Lokoja).

Exit mobile version