Connect with us

WASANNI

An Sake Sassaka Mutum-Mutumin Ronaldo A Portugal

Published

on

Hukumomi a kasar Portugal sun musanya mutun-mutumin zakaran kwallon kasar Cristiano Ronaldo da wani sabo wanda ke dauke da sunanshi a filin jirgin saman Madeira.
Sauya mutum-mutumin na zuwa ne sa’o’I kalilan bayan zakaran kwallon duniyar ya zurawa kasar tasa kwallo uku a wasan da suka buga da kasar Sipaniya a gasar cin kofin duniya da yake gudana yanzu haka a Rasha.
A shekarar 2013 ne dai aka sanya mutum-mutumin aka kuma sauya wani a shekara ta 2014 duk domin girmama gwarzon dan wasan kasar.
Rahotanni sun ce akwai gagarumin sauyi tsakanin tsohon mutum-mutumin da kuma sabon, inda yanzu wannan aka yi shi yana murumushi sabanin wancan na farko da ya murtuke fuska.
A baya dai mutum mutumin na Ronaldo ya fuskanci suka inda wasu ke kallonsa a matsayin cin fuska maimakon girmamawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: