Ibrahim Ibrahim" />

An Sake Zaben Aminu Shagali Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

Majalisar Dokokin Jihar kaduna, ta sake zaben Honarabul Aminu Shagali daga Karamar hukumar Sabon Garin Zariya a matsayin Sabon Kakakin Majalisar karo na biyu.

A yayin da ‘Yan majalisar suka zabi Honarabul Yusuf Zailani daga Karamar hukumar Igabi ta Yamma, wanda ya kasance a tsawon majalisar karo na hudu, a matsayin Mataimakin Kakakin Majalisa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin magatarkadar majalisar, Zubair Ibrahim, a yayin da yake rantsar da sababbin ‘yan majalisar dokokin jihar kaduna karo na shida.

An dai zabi shugabanin majalisar ne ba tare da wani hamayya ba.

Exit mobile version