Abba Ibrahim Wada" />

An Saki Ronaldinho Daga Kurkuku

 

An saki tsohon dan wasan kungiyoyin Barcelona da PSG, Ronaldinho, daga kurkuku, sannan an kuma yi masa daurin talala, bayan da aka tsare shi a kasar Paraguay sakamakon ya shiga kasar ta fasfo na jabu.

Zakaran kyautar Ballon d’Or na shekara ta 2005 ya yi zaman gidan kurkuku tare da dan uwansa ranar 6 ga watan Maris, inda aka zarge su da amfani da jabun fasfo sai dai tun farko an hana bayar da belinsu, amma yanzu an amince da biyan fam dubu 648,000 kowanne, sannan za su ci gaba da zama a kasaitaccen otal a birnin Asuncion kafin a gurfanar da su.

Ronaldinho mai shekara 40 da dan uwansa Roberto Assis sun musanta laifin da ake zarginsu sannan kuma Lawyansu ya kwatanta garkame su da aka yi da keta doka da cin zarafin da adam kamar yadda ya bayyana a wata hira da yayi baya an bayar da belin nasu.

Alkali Gustabo Amarilla ya ce kudin da aka bayar da su beli ya yi, kuma hakan ne zai tabbatar da ba za su tsere daga kasar ba kuma zasu ci gaba da zama a kasar har zuwa lokacin da za’a fara shari’arsu.

Shi dai Ronaldinho ya ziyarci Paraguay domin tallata littafi da yekuwar tallafawa yara marasa galihu kuma dan wasan wanda ya lashe kofin duniya a shekara ta 2002 ya buga wasa a kungiya da ta hada da Paris St Germain da Barcelona da AC Milan.

A shekarar 2015 dan kwallon ya yi ritaya, bayan da ya kammala wasa a kungiyar Brazil mai suna Fluminense sannan Ronaldinho wanda ya lashe kofin duniya a 2002 da Brazil, yana cikin ‘yan kwallon Fifa fitattu 11 na duniya a shekarar 2005 da kuma 2006.

Exit mobile version