An Samar Da Matakan Tsaro Bisa Jita-Jitar Ziyarar Sunday Igboho A Garin Ilori

Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

Garin Ilori, babban birnin jihar Kwara,a ranar Juma’ar da ta gabata ta shiga rudani biyo bayan matakan tsaron da aka samar a garin da kewayenta game da jita-jitar da ake ta yadawa na cewa jagoran ‘yan bangar Yarabawa nan, wato Sunday Igboho na shirin kawo ziyara birnin..
Jami’an tsaro, ciki har da sojoji  sun toshe dukkan hanyoyin shigowa babban birnin na jihar Kwara.
Haka kuma ‘yan sanda sun datse gaban hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar dake kan babban titin Ahmadu Bello da motocinsu, inda aka tilastawa ababen hawa dake zirga zirga akan hanyar dasu canja zuwa sauran hanyoyin dake birnin na Ilori.
Wakilin jaridar LEADERSHIP Ayau ya nakalto cewa samar da kwararran tsaron baya wuce nasaba da jita jitar da jama’a suka rika yadawa a dandalin sada zumunta ( Soshal Midiya)na cewa mai fafutukar kwato yancin yarbawa, Mista Sunday Igboho, na shirin kawo ziyara garin Ilori, babban birnin jihar Kwara.
Sai dai kuma mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Mista Okasanmi Ajayi yace” Kada jama’a su tsorata, babu abinda zai faru”.
Samar da tsaron yana daga cikin matakin da rundunar ta dauka domin kare jihar ta Kwara “.
Jama’a su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba” inji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan.

Exit mobile version