Umar A Hunkuyi" />

An Sami Ma’aikacin Kwalejin Kimiyya Ta Auchi Da Aka Sace A Mace

Wani ma’aikacin Kwalejin kimiyya da fasaha ta Auchi, Mista Samuel Okolie, wanda aka ce wasu ‘yan bindiga sun sace shi a ranar 9 ga watan Oktoba, an same shi a mace.

An sami Okolie ne a mace a gonarsa da ke garin Abiele, kusa da Auchi, a karamar hukumar Etsako ta yamma, wajajen Edo tun da sanyin safiyar ranar Lahadi.

An ce mutuwar ta Okolie ta faru ne makwanni biyu da mutuwar wani ma’aikacin makarantar, Dakta S. Okhikhena, wanda aka ce abokin Okolie din ne na kud-da-kud, wanda shi ma aka kashe shi ta irin wannan hanyar.

An ce an sace Okolie ne a kan hanyar sa ta zuwa gonarsa bayan da ya tashi daga aiki domin ya kwaso mutanan da suke yi masa aiki a gonar na shi.

An ce an jefar da gawar na shi ce wacce aka yi wa gunduwa-gunduwa a kusa da wata babbar motar da yake tukawa a lokacin da ‘yan bindigar suka sace shi.

Amma Kwamishinan ‘yan sanda da ke Edo, Mista Danmallam Mohammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin cewa yay i Okolie ba sace shi ne aka yi ba.

Mohammed ya ce, mutuwar tana iya kasancewa ta ya kashe kansa ne kasantuwar yanda aka sami gawar sa an jike ta da ruwan Acid.

“A gaskiya lamarin na ya kashe kansa ne, domin ba wani abin da aka dauka daga gare shi ko kuma motarsa.

Sai dai Kwamishinan ya ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da abin da ya kai ga mutuwar ta Okolie.

Exit mobile version