Umar A Hunkuyi" />

An Samu Asarar Rayuka Biyu A Zaben Cike Gurbin Kogi

‘Yan sanda a Lokoja sun tabbatar da karin mutuwar mutum guda ranar Asabar, a zaben cike gurbin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Lokoja da Kogi, a majalisar tarayya.

Kakakin rundunar, William Aya, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa a Lokoja a ranar ta Asabar, inda ya ce, hakan ne ya kawo adadin mutanan da aka kashen zuwa biyu a lokacin zaben.

Ya ce, na baya-bayan nan, wanda ya ce sunan sa Yadau Umoru, an kashe shi ne a rumfar zabe ta Unguwar Pawa, wacce take a kofar fadan maigarin, a lokacin da yake kokarin kwace akwatin zabe.

A cewar sa, gawar mamacin tana dakin ajiye gawarwaki na cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Lokoja.

Tun da farkon ranar an kashe wani da ba a iya tantance ko wane ne ba a rumfar zaben da ke gaban ofishin hukmar raba hasken lantarki ta Abuja, da ke Lokoja, a lokacin da shi ma yake kokarin ya kwace akwatin zaben.

An dai fara gudanar da zaben ne lami lafiya, inda mutane da yawa suka fito domin yin zaben, daga baya ne lamarin ya kazance sabili da yadda aka yi ta siyan kuri’u da kuma fisge akwatunan kada kuri’un.

Exit mobile version