’Yan Jarida">

An Samu Fahimtar Juna Tsakanin ’Yan Jarida Da Ofishin Mataimakin Gwamnan Bauchi

Mambobin kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Jihar Bauchi (Correspondents’ Chapel) sun samu daidaito da ofishin mataimakin gwamnan jihar Bauchi kan matakin da suka dauka tun da fari na kaurace wa nakalto labaran harkokin ofishinsa.

Idan za ku iya tunawa dai, bayanai sun fita kan cewa kungiyar ta dauki matsayar kaurace wa daukan labaran harkokin da suka shafi ofishin mataimakin gwamnan, Sanata Baba Tela, inda suka danganta hakan da rashin gamsuwa da matakin da ya nuna musu na rashin karamci yayin da suka je daukar wani rahoto a ofishinsa.

Sai dai a sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar a jiya ta hannun sakatarenta, Mista Samuel Luka, ta shaida cewar an samu fahimtar junan ne bayan da kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Garba Dahiru da Kakakin gwamnan jihar Bauchi, Kwamared Muktar Gidado suka shiga cikin lamarin cikin gaggawa domin shawo kan rashin jituwar da aka samu.

Luka ya ce, sakamakon wani zama da jagororin kungiyar da suka yi, an samu cimma matsaya da shawo kan lamarin cikin lamuma da salama ba tare da kai ruwa-rana ba.

“Jagororin Chapel sun kai ga daukan matakin ne bayan ganawar fahimtar juna da suka yi da wakilan gwamnati, jagororin Chapel da mambobinta sun amince da cewa yanzu za su dawo cigaba da daukan labaran ofishin mataimakin gwamnan domin cigaban jihar da kuma neman kyautata zaman lafiya,” inji sanarwar.

“Kan wannan matakin, mambobin wakilan kafafen sadarwa za su cigaba da daukan labaran da suka shafi harkokin ofishin mataimakin gwamnan,” inji sanarwar.

 

Exit mobile version