Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,
An samu karancin fitowar jama’a a zaben shekarar 2021 na Kananan Hukumomi 23 da Kansiloli da Hukumar Zabe ta Jiha ke aiwatarwa yau a Sakkwato.
A Bodinga, Shagari, Tambuwal, Wamakko, Sakkwato ta Arewa da Sakkwato ta Kudu da wakilinmu ya shaidi gudanar da zaben an samu karancin fitowar jama’a sosai lamarin da jama’a da dama suka bayyana a dalilin kasancewar zaben na jam’iyya daya kacal, domin kananan jam’iyyun da suka shiga ba su da wani tasiri.
An gudanar da zaben ne ba tare da wata hamayya ba kasancewar jam’iyyar adawa ta APC ta kauracewa zaben ba tare da shiga ba tare da kawo hujjar rashin gamsuwa da tsare-tsaren zaben, lamarin da PDP da ke mulkin Jihar ta kira soki burutsu tare da ayyana rashin shigar APC a zaben a dalilin hango faduwa kasa warwas a bisa ga kima da daukakar PDP da dawowa daga rakiyar APC da aka yi a dalilin rashin kyakkyawan shugabancin Muhammadu Buhari.
Jama’a da dama ba su fito a rumfunan zaben ba, hasalima saboda rashin jama’a da yadda jama’a suke ci-gaba da gudanar da harkokin su tamkar ba zabe ake aiwatarwa ba. Masu sana’o’i daban-daban sun bude kasuwancinsu, haka ma a na zirga-zirga kamar ko wace irin rana ciki har da ‘yan achaba da motocin kasuwa.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal wanda ya jefa kuri’a a rumfarsa ta Kofar Ajiya 001 a Tambuwal ya bayyana cewar a bisa ga sanin muhimmancin da ke ga matakin Karamar Hukuma wajen kyautatawa al’ummar karkara ne dalilin da yasa Gwamnatinsa ta bayar da himma wajen ganin an samu nasarar aiwatar da zaben ta hanyar bayar da dukkanin cikakken goyon bayan da ya kamata ga Hukumar Zabe ta Jiha.
Gwamnan ya bukaci wadanda suka samu nasara, su rungumi jama’a su yi masu ayyuka tare da adalci a shugabancin su, haka ma ya bukaci wadanda suka sha kasa su rungumi kaddarar faduwa zabe.