Khalid Idris Doya" />

An Samu Koma-baya Kan Yaki Da Korona A Bauchi

Hukumomin lafiya a jihar Bauchi sun shaida cewar a sakamakon gwajin cutar Korona da suka yi wa al’umma a kwana guda sun tabbatar tare da gano mutum sittin da tara (69) na dauke da cutar.

Alkaluman da suka fito daga hukumomin lafiya a daren ranar Talata na tabbatar da adadi mafi tsoka da suka kamu da cutar a tarihin annobar Korona a jihar ta Bauchi. Wannan matakin shine irinsa na farko da aka samu faruwarsa a jihar tun lokacin da annobar ta barke.

Hakan na nuni da koma baya da aka samu a yaki da cutar ta Korona, sai dai hukumomin lafiya da gwamnatin jihar sun sha alwashin sake jan damara domin dakile bazuwar cutar ta Korona a jihar.

Bayanin wadda ya ke kunshe a rahoton kullum da ma’aikatar lafiya ta jihar ke fitarwa domin shaida wa jama’a halin da ake ciki, bayanin ya nuna cewa an gudanar da gwajin tare da tabbatar da adadin masu dauke da cutar ne a dakin gwaje-gwajen cutuka da ke Bauchi.

A kan wannan matakin, kawo yanzu haka jihar Bauchi tana da mutum 131 da su ke kan jinyar cutar a daidai lokacin da mu ke ciki.

Rahoton na cewa; ya zuwa ranar Talata, 9 ga watan Yuni 2020, sun samu adadin wadanda suka kamu da cutar mafi yawa a tarihin wannan annoba a jihar Bauchi.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ta shaida cewar kawo shekaran jiya Talata mutum 364 aka tabbatar sun kamu da cutar tare da sallamar wasu ba’adin da suka warke, sai kuma mutum 131 da yanzu haka su ke jinyar cutar a kwance a cibiyar killacewa, “Zuwa yanzu, mun dauki samfurin mutum 2,478 tun bayan barkewar cutar a jihar, bincike ya tabbatar da cewar mutum 364 ne suka kamu da cutar a jihar Bauchi, amma tunin muka sallami mutum 224 bayan sun warke daga cutar.”

Hukumar lafiyar ta kuma sanar da cewa mutum goma ne cutar ta kashe a dukkanin fadin jihar tun lokacin barkewarta zuwa ranar Talatar da ta gabata.

Exit mobile version