Ahmad Muhammad Dan Asabe" />

An Samu Naira Miliyan 1,786,500 Cikin Motar Da Ta Yi Hadari A Lakwaja

Pic.10. A Scene of Accident at Asolo Bus Stop, Itowolo village, Ikorodu in Lagos on Monday (23/7/18). 03945/23/7/18/Babatunde Atolagbe/NAN

A ranan Talata ne Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) a jihar Kogi, ta mayarwa da matar wani da ya yi hadari da mota naira miliyan 1,786,500.
Da yake bai wa matar kudin, shugaban hukumar ta Road Safety a jihar, Mista Emmanuel Abe, ya shaida wa Madam Charity cewar, an samu kudin ne a cikin motar mijinta da ya yi hadari. Shugaban ya bayyana cewa, mutumin ya yi hadarin ne a cikin wata mota kirar bus mai lambar Abuja KWL 386 YH, lokacin da hadarin ya faru a daidai kauyen Gegu dake kan babban hanyar Lokoja zuwa Abuja da misalin karfe 2,30 na rana.
Ya ci gaba da bayanin cewa, jami’ansa sun samu kiran waya kwatsam, koda suka isa wurin da abin ya faru, sun samu shi kadai ne cikin motar lokacin da hadarin ya auku, sun same shi a ya bugu sosai, bai ma san inda yake ba. Isar wurin, sai su ka yi gaggawar garzayawa da shi wata asibiti mafi kusa, kuma lokacin ci gaba da duba motarsa ne, aka samu wadannan kudaden ciki.”Inji Shi “.

Exit mobile version