Rahotanni daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sun ce an samu rarrabuwar kai tsakanin ‘yan wasan kungiyar, dangane mayar da dan wasan kungiyar, dan kasar Jamus, Mesut Ozil cikin tawagarsu a watan Janairu mai kamawa.
A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniya za ta kare tsakanin Arsenal da Ozil dake karvar albashin fan dubu dari uku da hamsin 350, a mako guda, wanda kuma duk da hakan kocin kungiyar Mikel Arteta ya cire shi daga tawagarsa dake buga wasannin Premier da kuma Europa a bana.
Sai dai majiyoyi daga kungiyar sun ce a watan Janairu ake sa ran maida Ozil cikin tawagar da a baya aka maida shi saniyar ware, sakamakon fama da matsalar rashin kwararren dan wasan tsakiya a kungiyar.
Koda yake wasu na ganin abin da kamar wuya domin da zarar an bude kasuwar sauyin shekar ‘yan wasan, yana da damar raba gari da kungiyar ta Arsenal saboda kungiyoyi da dama suna neman ya sanya musu hannu.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar suna goyon bayan a mayar da Ozil cikin tawagar domin zai taimakawa kungiyar duba da halin da suke ciki a yanzu na rashin samun nasara wadda kuma aka alakanta hakan da rashin kwararre wajen sarrafa kwallo kamar yadda Ozil din ya keyi.
Sai dai wasu kuma suna ganin shigowar dan wasan a cikin watan Janairu bata da amfani saboda tuni an shirya kakar wasa ta bana babu shi kuma alakar dan wasan da kociyan kungiyar bata da kyau hakan yasa suke ganin idan ma ya dawo buga wasa babu tabbas idan zai samu damar buga wasanni akai-akai sannan kuma zaiyi wahala idan zai iya bawa kungiyar abinda take bukata.
Rikicin Ozil da Arsenal dai ya samo asali ne tun a lokacin tsohon kociyan kungiyar, Unai Emery sannan kuma Arteta shima yazo ya dora duk da dai wasu suna ganin manyan shugabannin kungiyar ne suke da ruwa da tsaki akan rikicin dan wasan da kungiyar.
Ozil dai ya koma Arsenal daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid akan kudi fam miliyan 42 kuma tun zuwansa ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar cin kofin kalubake na FA sannan sunje wasan karshe na gasar Europa kafin Chelsea ta doke su a wasan karshe.