Connect with us

LABARAI

An Samu Raguwar Mutuwar Alhazan Nijeriya Fiye Da Koyaushe A Bana

Published

on

Kwamishinan da ke shugabantar harkokin lafiya na hukumar jin dadin alhazai ta kasa, Dakta Ibrahim Abubakar Kana ya shaida cewar kawo yanzu Alhazan Nijeriya 12 ne suka rasu a lokacin gudanar da aikin hajjin wannan shekarar ta 2018 a kasa mai tsarki.

Dakta Kana ya shaida hakan ne a lokacin da suke ganawa da hukumar NAHCON da jami’an hukumar jin dadin Alhazai na jahohi a birnin Makkah ta kasar Saudiyya a ranar Laraba.

Ganawar ta yi bayanin yanayin da alhazan Nijeriya suka kasance a ciki gabanin da kuma bayan gudanar da aiyukan aikin hajjin wannan shekarar dangane da sha’anin lafiya.

Ya kara da cewa a wannan shekarar ba su fuskanci wasu manyan kalubale ba ta fuskacin kula da lafiyar alhazai, ya shaida cewar hakan ya biyo bayan jajircewar da suka yi domin tabbatar da bayar da kula ga lafiyar alhazan Nijeriya ne. Sakamakon hakan, aikin Hajjin wannan shekarar ya kasance mafi karancin rasa rai a tarihin Nijeriya.

“Tawagar sashin kula da lafiya na tarayya ba za su bar gudanar da aikinsu bar har sai dukkanin alhazan Nijeriya sun bar kasa mai tsarki zuwa gida Nijeriya. Za mu ci gaba da aikin bayar da kula ta fuskacin lafiyar maniyyata,” In ji Kwamishinan

Kwamishinan ya daura da cewa, sun kafa kwamitocin sanya ido da bibiyar asibitoci, cibiyoyin lafiya da sauran wuraren kula da lafiyar Alhazan Nijeriya domin tabbatar da yanayin da alhazan ke ciki na tafi daidai yadda sha’anin lafiya ke da bukata.

Ya kuma kara da cewar cibiyoyin lafiyar mallakinsu da ke Madina an sake bude su domin kula da alhazan Nijeriya masu ziyartar garin na Manzon Allah.

Ya bayyana cewar alhazan Nijeriya 12 da suka rasu a can kasa mai tsarkin sun rasu ne a sakamakon dalilai daban-daban.

Ya bayyana cewar suna shirin kyautata aikinsu a shekara mai zuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: