An Sanya Siyasa A Batun Amotekun- Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya nemi zama da gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma da kuma Ministan Shari’a na kasar, Mallam Abubakar Malami, don tattaunawa kan batun Amotekun, inda ya ce akwai matsalar rashin fahimtar tsarin.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Bola Tinubu da aka aike wa manema labarai, ya ce kafa kungiyar tsaron ta Amotekun sam-sam ba barazana ba ce ga kasar tun bayan da gwamnonin yankin suka kafa ta, a kokarinsu na magance matsalar tsaro a jihohinsu.

A cewar sanarwar “batun Amotekun ya karade ko ina kuma ya ja hankalin kafafen yada labarai, ya shafi yadda gwamnatoci za su taimaka wajen bai wa al’umominsu tsaro.

“Wannan abun damuwa ne sai dai kuma an sanya siyasa cikinsa.”

Tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce “wadanda suke ikirarin gwamnatin kasar na neman dankwafar da Kudu Maso Yamma ne, kawai ra’ayinsu suke fada.”

A baya-bayan nan ne gwamnatin Nijeriya ta soke kungiyar tsaro ta Amotekun da wasu jihohin shiyyar kudu suka samar.

Tun bayan daukar wannan mataki dai, jama’a a kasar ke tofa albarkacin bakinsu game da lamarin inda wasu ke ganin matakin wani koma baya ne, kuma yana iya zama matsala a kasar nan gaba.

Exit mobile version