Umar A Hunkuyi" />

An Sayar Da Mutane 20 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Matsayin Bayi

Akalla mutane 20 ne da aka yi garkuwa da su a Jihar Katsina, aka bayar da rahoton cewa an siyar da su a matsayin bayi a kasar Burkina Faso.

Rahotanni sun nuna cewa mutanan an sato su ne daga karamar hukumar Kankara, ta Jihar ta Katsina, sannan sai aka siyar da su ga wata mata a Kwatano, wacce ita kuma ta siyar da su ga wani dan kasuwa mai siyan bayi domin aikin bauta a kasar ta Burkina Faso.

In dai ba a manta ba, Gwamnan Jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari, ya kaddamar da wani shiri na tattaunawa domin samar da zaman lafiya a lokacin da ya ziyarci maboyan ‘yan bindigan ya kuma zauna da su har ya kulla wata yarjejeniya da su wacce a karkashinta aka sako wasu da aka yi garkuwan da su da kuma wasu masu yin garkuwa da mutanan da suke tsare a hannun hukuma.

Wata tabbatacciyar majiya ta labarta mana cewa, Gwamnan ya bincika da gano wajen da aka siyar da mutanan Jihar ta Katsina su 20 a can kasar ta Burkina Faso, har ma ya kaddamar da wani shiri na ceto mutanan da aka siyar din daga zama a cikin yanayi irin na bautan wannan zamanin a can kasar ta Burkina Faso.

Majiyar ta ce, har ma mai baiwa Gwamnan shawara a kan muggan kwayoyi da fataucin mutane, Alhaji Hamza Brodo, ya tafi kasar ta Burkina Faso domin tattaunawa a kan yanda za a sami ‘yanto mutanan.

Da yake tabbatar da aukuwan hakan, Brodo cewa ya yi, Tabbas zan tafi kasar ta Burkina Faso a karshen makon nan.

“Domin na sani ko da gaske ne mutanan da aka siyar din ‘yan asalin Jihar ta Katsina ne, bayan na sadu da su da kuma wadanda suke rike da su din,” in ji Brodo.

Exit mobile version