An Shawarci Gwamnati Da Ta Kulle Duk Kafofin Yada Labaran Da Ba Sa Biyan Albashi

Kiev, Ukraine - October 17, 2012 - A logotype collection of well-known social media brand's printed on paper. Include Facebook, YouTube, Twitter, Google Plus, Instagram, Vimeo, Flickr, Myspace, Tumblr, Livejournal, Foursquare and more other logos.

Daga Umar A Hunkuyi

Kungiyar ma’aikatan gidajen yada labarai ta kasa, NPC, ta shawarci gwamnatin tarayya da ta ayyana cewa, kin biyan ma’aikatan yada labaran albashi babban laifi ne.

Kungiyar ta ce, hakan zai inganta yadda jami’an yada labaran za su rika bayar da labaran zabe a kasarnan.

Babban sakataren kungiyar, Nnamdi Njemanze, ne ya bayar da wannan shawarar ranar Litinin cikin wata sanarwan bayan taron kwanaki biyu kan sanin yadda za a inganta aikin bayar da labaran zaben, wanda kungiyar ta yi a Akure,ta Jihar Ondo.

Sakataren ya ce, mahalarta taron sun lura da cewa, ‘Yan jarida sun zama tamkar wata haja a hannun ‘yan siyasa ne saboda rashin kyautata ma su da ake yi, da kuma yadda ake nuna ma su bambancin yanayi, kabilanci ko Addini.

Ya karfafa bukatar masu gidajen yada labaran da su tabbatar da su na biyan ma’aikatan su albashin su da sauran kudaden alawus din su a kan kari domin su rage ma su wahalhalun su.

Ya kuma bukaci masu gidajen yada labaran da su yi sana’ar na su domin ci gaban kasa, su kuma guji sanya kabilanci ko bambancin Addini a cikin sana’ar na su.

Hakanan taron ya bayar da shawarar kungiyar ma’aikatan yada labaran, NPC, da ta sanya karancin kyautatawan da za a yi wa ma’aikatan yada labaran, ta kuma nemi a kafa dokar kasa a kan hakan.

Taron kuma ya bukaci Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ta samar da riguna na musamman da aka rubuta, PRESS, a jikin su ga dukkanin manema labaran da aka yarje masu da su kawo rahotannin zaben a ranakun zabe.

Sakataren kuma ya shawarci gwamnati da ta tabbatar da an hukunta ‘yan jaridun karyan da aka kama a lokutan zaben domin raba sana’ar masu kawo rahotannin da baragurbi.

Hakanan kuma, taron ya bukaci ‘yan jaridun da su kare kansu da yin biyayya ga dokokin aikin na su, da kuma tsarin mulkin kungiyar ‘yan jaridu ta kasa, NUJ, domin haskaka masu aikin na su.

Sakataren ya ce, taron ya yi fatali da wani yunkuri da aka yi na samar da wata doka da za ta kula da kafafen yada labarai na yanar gizo da kuma yin jawaban da ba su kamata ba, taron ya ce, matukar aka yi aiki da dokokin da ake da su yanzun haka, duk za su magance matsalolin.

Akalla mutane 52 ne suka halarci taron bitan, 36 ‘yan jaridu ne daga sassan jarida da rediyo da talabijin.

 

Exit mobile version