Connect with us

MANYAN LABARAI

An Shawarci Iyaye Mata Yadda Zasu Yi In Yara Kanana Sun Ci Guba

Published

on

Dakta Victor Fayemi ya shawarci iyaye mata da su daina sa yara kanana aman dole a yayin da suka ci abinci mai guba ko suka hadiye kwayoyin magani, ko suka sha maganin ruwa fiye da kima.

‘Yara kanana zasu iya hadiyar magunguna masu hatsari ba tare da sun sani ba, ko su ci abinci mai dauke da sinadari mai cutarwa, wanda yakamata iyaye su kula sosai wajen ajiye su.’ Inji Dakta Fayemi

Ya kara da cewa: Lokuta da dama ana kawo yara kanana da suka sha abubuwa masu cutarwa, misali kananzir, sabulu, maganin kwari, fiya-fiya da sauran irin wadannan sinadarai masu hatsari ga lafiyar dan adam, wadanda yakamata ace ana ajiye inda yara kanana ba zasu iya risker su ba.

An shawarci iyayen da su daina ajiye kananzir da duk wani abu mai illa a cikin robobin abin sha, saboda yaran basu da hankalin da zasu tantance abin sha ne ko abune mai hatsari gare su.

‘Sanya yara su yi amai da karfi ba daidai bane, in irin wannan lamarin ya faru, toh iyaye su yi maza su garzaye da yaro asibiti don kwararru su yi abinda ya dace a kan lokaci.’ Inji Daktan

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: