An Shawarci Masu Kada Kuri’a A Zaben 2019

Ganin yadda ake kara tunkarar zaben 2019 yasa manyan ‘yansiya da kanana tare da ‘yan kasuwa da masu son kawo canji mai anfani ga al’umma, suka fara kiraye-kiraye da bayar da shawarwarin cewa lallai a tabbatar an zabi wadanda zasu kawo ci gaba musamman masu kishin al’umma da rike amana da sauransu.
Shawara na baya bayan nan ya fito ne daga bakin wani matashin dan siyasa kuma dan jam’iyyar APC daga mazabar unguwar Kawaji a Karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Hon. Sabo Muhammad Dankwara wanda da aka fi sani da suna Sabo Dankwara, a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya a ofishinsa dake unguwar Dakata.
Ya ce, zaben na 2019 ya banbanta da sauran zabukan shekarun baya musamman wajen zaben shuabanni nagari masu kishin al’umma da kuma kawo canji masu ma’ana. Dankwara ya bukaci masu kada kuri’a a zaben dake tafe dasu kaucewa zaben shugabanni marasa kishin al’umma sai dai kawai kishin aljuhunsu.
Ranakun zabe kuma a guji tayar da hankula musamman bayan sanar da zaben shugaban kasa, ya ba da misalin yadda aka samu hatsaniya a zabukan baya wajen sanar da zaben shugaban kasa. Ganin ana daf da fara yakin neman zabe kuwa ya jawo hankulan ‘yan takara dasu guji furta kalaman da za su tayar da hankulan al’umma.
Ya yi amfani da wannan dama na yin kira ga sababbin shugabannin jam’iyya APC da aka zaba kwanakin baya, ya shawarcesu dasu kwatanta gaskiya da tsoron Allah wajen tafiyar da shugabanci, musamman wajen hada kan ‘yan APC wuri daya domin tunkarar zabukan da ke tafe, na 2019

Exit mobile version