Balarabe Abdullahi" />

An Shawarci Musulmi Da Su Ci Gaba Da Ibada Bayan Azumi

Muslim man using misbaha to keep track of counting in tasbih

An shawarci al’uumar musulmi a duk inda suke a Nijeriya da kuma sassan duniya, da su ci gaba da rungumar ibada, fiye ma da yadda suka yi a watan Azumin day a gabata.

Babban sakaare na Hadaddiyar kungiyar musulmi ta Nijeriya [ UNITED FOUNDATION], Shekh Sufyan Saleh Algarkawy,ya bayar da shawarar a madadin shugaban kungiyar, Shekh Malam Rabi’u Abdullahi Ganganfa, wanda kuma har ila yau, shi ne shugaban kungiyar Fitiyanul Islam reshen jihar Kaduna.

Shekh Sufyan Algarkawy ya ci gaba da cewar, babu ko shakka a kwai al’uumar musulmi da yawan gaske da suke aje batun yin ibada da zarar watan azumi ya wuce, wannan a cewarsa, babbar matsala ce day a kamata al’ummar musulmi su yi karatunta – natsu a kan wannan matsala.

Ya ci gaba da cewar, lokaci ya yi ga duk wani musulmi da ke da wannan mummunar hali, na aje ibada da zarar an kammala watan azumi, da su canza halin da suka runguma, domin su sami ci gaban da zai zama ma su alheri tun a nan duniya, ya zuwa gobe.

Shekh Algarkawy ya kuma nunar da cewar,in har mutum ya fahimci lokacin watan azumi ne kawai zai kyautata alakarsa da ubangiji, to, a cewa Shehin malamin, wannan babbar kuskure ne da ke bukatar gyara a kan lokaci da musulmi day a rungumi wannan hanya ya dauka, bay a ci gaba da bin wannan hanyar ba.

Da kuma Shekh Sufyan Algarkawy ya juya ga takwarorinsa malamai kuma, musamman wadanda ke aje batun wa’azi da kuma fadakarwa, a dalilin kammala watan azumi, sai ya tunatar da ire – iren wadannan malamai da su canza shawara, su kara tashi tsaye, domin sauke nauyin da mai duka ya dora ma su, na ilmantar da al’umma, ba sai a watan azumi kawai ba.

A karshen ganawar da aka yi da babban sakataren wannnan kungiya, ya yi kira ga daukacin al’ummar musulmi da su fahimci, hadin kai shi ne mafita duk matsalolin da suke addabar musulmi, a sassan duniya, ba Nijeriya kawai ba, sai ya ce, wannan ne ya sa aka kafa wannan kungiya, domin hada kan al’ummar musulmi da kuma yi wa musulunci aiki a daukacin Nijeriya, ba a arewacin Nijeriya kawai ba

Exit mobile version