Daga Abba Ibrahim Wada
An shiga rana ta biyu ta zaman makoki na tsawon kwanaki uku a kasar Argentina domin jimamin mutuwar tsohon tauraron dan kwallon duniya, Diego Maradona wanda ya yi ban-kwana da duniya a ranar Laraba, yana da shekaru 60 sakamakon bugun zuciya.
Tuni aka shinfide gawarsa a katafaren ginin Casa Rosada da ke fadar shugaban kasar Argentina domin bai wa jama’a damar ganawa ta karshe ga dan wasan kuma yanzu haka daruruwan mutane sun fara jeruwa a kan layi don ganin gawar tasa daya-bayan-daya.
Tuni aka dage wasa tsakanin Sport Club International da kuma tsohuwar kungiyar Maradona wato Boca Juniors domin karramawa ga marigayin sannan masoyansa sun yi dafifi a filin wasa na Boca Juniors da ke birnin Buenos Aires, inda akasarinsu ke ta rusa kuka shame-shame saboda bakin cikin mutuwarsa.
Maradona ya buga wasa a kungiyoyin kwallon kafa irinsu Barcelona da Napoli, sannan shi ne kyaftin din tawagar Argentina wadda ta lashe kofin duniya a shekarar 1986, inda a wancan lokacin aka zarge shi da yin amfani da hannu wajen jefa kwallo a ragar Ingila a matakin kwata fainal na gasar.
Maradona ya mutu ne makwanni da yi masa tiyata a cikin kokon kansa sakamakon daskarewar jini a kwakwaluwarsa, sannan ya yi fama da masifar kwankwadon barasa da hodar ibilis kodayake mai shigar da kara na gwamnatin Argentina ya ce, za a gudanar da gwajin kan gawarsa.
Tuni tsoffin ‘yan wasa har ma da wanda ke kan ganiyarsu suka fara aikewa da sakon ta’aziyar rashin Maradona, inda Pele da ake kallo a matsayin babban abokin hamayyarsa ya ce, yana fatan za su hadu wata rana a lahira domin buga wasa.