An Shigar Da Korafin ’Yan Sanda Guda 1,247 A Jihohi 30

Ma’aurata

Kimanin makonni biyar bayan da hukumar tattalin arziki ta kasa (NEC), karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta ba da umarnin kafa kwamitin shari’a a duk fadin kasar nan, don bincikar korafe-korafen da ake yi na zargin ‘yan sanda da cin zarafin jama’a da kuma aikata kisan kai ba bisa doka ba, fiye da jihohi 30 da Babban birnin tarayya (FCT) sun yi biyayya ga wannan umarnin a inda su ka samu sama da rubutacciyar kara 1,247.

Rahoto ya tattara cewa, Jihohin Kano, Kebbi, Sokoto, Zamfara, Borno da Yobe har yanzu ba su kafa kwamiti a jihohin su ba. Rahoton ya nuna cewa, korafe-korafe sama da 200 da kwamitin FCT ta karba sun fito ne daga wadanda zanga-zangar #EndSARS ya shafa.

Hukumar ta NEC, a wani taron da ta gudanar a watan jiya wanda gwamnoni suka halarta a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Osinbajo, ta umarci kafa kwamitocin ne don yin adalci ga duk wadanda ke fama da rudanin runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS) da sauran rundunonin ’yan sanda.

Kwamitocin shari’ar, wadanda za a kafa a duk jihohin, za su kunshi wakilan matasa, dalibai, kungiyoyin farar hula, kuma alkalin da ya yi ritaya ne zai shugabanta.

A jihar Abia, kwamitin shari’a mai mambobi 21, karkashin jagorancin Justice Sunday Imo, wani babban alkalin jihar mai ritaya, ya zuwa yanzu ya karbi korafe-korafe akalla 100. Alkalin wanda ya tabbatar da yawan koke-koken, ya ce, kwamitin ta tsayar da gobe a matsayin ranar da za a gabatar da kararrakin.

A jihar Adamawa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shi ma ya kafa kwamitin alkalai 11 a jihar, karkashin jagorancin Mai Shari’a Adamu Hobon.

Sakataren kwamitin, Mista Usman Suleiman, ya ce kwamitin ta fara zama a makon da ya gabata kuma ta karbi koke-koke har sau biyar.

A jihar Taraba, kwamitin da gwamna Darius Ishaku ya kafa tuni ta fara zama a Jalingo, babban birnin jihar. Shugaban kwamitin mutum 10, Mai Shari’a Christopher Awubra, ya tabbatar da karbar koke-koke 11 daga jama’a.

Biyo bayan jerin zarge-zargen take hakkin bil adama da jami’an rundunar SARS suka yi, gwamnan jihar Enugu, Hon. Ifeanyi Ugwuanyi, ya kaddamar da kwamitin mutum takwas, kuma ya zuwa yanzu ta karba korafe-korafe 30.

A jihar Delta karkashin jagorancin, Justis Celestina Ogisi shima ya samu korafe-korafe kusan 15, a cewar wani mamban kwamitin. Sai dai, ba kamar sauran kwamitocin shari’a ba, wadanda ke da wa’adin watanni shida, Sakataren kwamitin, Omamuzo Erebe, ya ce kwamitin shari’ar na da watanni uku daga ranar da aka kaddamar da ita don gabatar da rahoton ta.

A jihar Kuros Riba, kwamitin mutum bakwai, karkashin jagorancin Mai Shari’a Michael Edem, sun karbi korafe-korafe 54. Da jin wadannan koke-koken ne kwamitin ta gabatar da ranar 26 ga Nuwamba don ba wa ‘yan sanda damar amsa tambayoyi.

Shugaban kwamitin a jihar Ribas, Mai Shari’a Chukwuneye Uriri, ya ce, ba daidai ba ne a bayyana yawan koke-koken da aka karba kafin fara aikin kwamitin. Hukumar ta sanya gobe don fara aikin ta a Fatakwal. Zaman taron jama’a zai dauki tsawon wata daya. Bugu da kari, Rahoto ya tattaro cewa, hukumar ta karbi korafe-korafe da dama kuma lauyoyi da dama sun shirya gabatar da karar wadanda abin ya shafa a gaban kwamitin.

Shugaban kwamitin na Jihar Ogun, Mai shari’a Solomon Olugbemi, ya ce, adadin koke-koken da suka karba daga wadanda ‘yan sanda suka zalunta, take hakkin dan adam da sauran laifuka masu nasaba da mutum 40.

Kwamitin mai mambobi 11, wanda Gwamnan Jihar Oyo, Mista Seyi Makinde ya kaddamar kwanan nan, ta karbi koke-koke 50, a cewar wata majiya ta kusa da Mai Shari’a Badejoko Adeniji da aka zaba.

Majiyar ta fada wa manerma labarai cewa, ba a sanya takamaiman ranar da kwamitin zai fara zama ba, inda ta kara da cewa kwamitin na daukar lokacin sa don yin cikakken aiki.

Kwamitin na Jihar Benuwai, wanda ya fara zamansa, ya karbi jimloli guda 28 daga wadanda abin ya shafa. Kwamitin, wanda Gwamna Samuel Ortom ya kafa, kuma karkashin jagorancin Justice Adam Onum (mai ritaya), yayi tsawon watanni shida.

Kwamitin ministoci na mutum 14 na Babban birinin tarayya da aka kafa domin tantance yawan asarar da barnar da ‘yan kasuwa da mutane suka yi yayin zanga-zangar #EndSARS ta karbi koke-koke sama da 200. Kwamitin, wanda Ministan Babban birnin tarayya, Malam Muhammed Bello ya kaddamar, karkashin jagorancin shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta FCT (FEMA), Mista Abbas Idris, shi ne ya gano iyalan wadanda aka kashe yayin rikicin da kuma tantancewa da sanya kima ga dukiyoyin jama’a da na masu zaman kansu da aka lalata.

A jihar Gombe, kwamitin shari’a mai mambobi 11 da Gwamna Muhammad Yahaya ta bude, kuma karkashin jagorancin Mai shari’a Sa’ad Mohammed, sun samu korafe-korafe biyar ya zuwa yanzu.

Kwamitin jihar Akwa Ibom karkashin jagorancin mai shari’a, Ifiok Ukana, ya zuwa yanzu ya karbi koke-koke har sau 92 daga jama’a don su duba. Kwamitin mutum takwas din suna da watanni uku don gabatar da rahotoninsu, sabanin sauran kwamitoci a mafi yawan jihohi, tare da wa’adin watanni shida.

A jihar Anambra, kwamitin da Justis Beronica Umeh ke jagoranta ya kabbi koke-koke 114. Gwamna Willie Obiano ya sanar da cewa, an ware zunzurutun kudi har Naira miliyan 200 domin biyan diyya ga duk wadanda suka gamu da cin zarafin ‘yan sanda a jihar.

A Jihar Nasarawa kuwa, Shugaban kwamitin mutum takwas, Mai Shari’a Badamasi Maina, ya tabbatar da cewa kwamitin nasa ta karbi koke har 16, ya zuwa yanzu, yayin da takwararta a Jihar Osun karkashin jagorancin Mai Shari’a Akin Oladimeji ke karbar korafe-korafe shida tun bayan kaddamarwar da Gwamna, Adegboyega Oyetolam, ya yi.

Kwamitin jihar Edo kuwa, wanda Gwamna Godwin Obaseki ya kaddamar, ya ce, ya karbi korafe-korafe kusan 70 tun lokacin da ya fara zama makonni biyu da suka gabata. Shugaban kwamitin mutum 20, Mai shari’a Ada Ehigiamusoe, ya bukaci duk wadanda abin ya shafa da su gabatar da koke-kokensu a ranar ko kafin ranar 29 ga Nuwamba.

Bincike a jihar Katsina wanda Gwamna Aminu Masari ya kaddamar, ya samu koke-koke har guda 61. Shugabanta, Mai Shari’a Abbas Bawale, ya tabbatar a karshen mako cewa a ranar litinin da ta gabata kwamitin zai fara sauraron kararrakin. Ya ce kwamitin zai fara sauraron ra’ayoyin jama’a ne daga yankin Funtua inda akasarin koke-koken suka fito da yawa.

Ya kara da cewa, daga nan kuma za a koma sauraren karar zuwa shiyoyin Katsina da Daura. Ya ce, “A yanzu haka, muna da koke-koke guda 56 daga shiyyar Funtua na jihar da kuma korafi biyar daga shiyyar Katsina. Muna jiran karin koke-koke daga yankin Daura. A yanzu, muna da jimloli guda 61 a dukka gaba daya.”

Kwamitin binciken jihar Imo ta tabbatar da karbar korafe-korafe guda 92. Kwamitin mai mambobi 16 tana karkashin jagorancin mai shari’a Florence Duroha-Igwe.

A jihar Ondo kuma, kwamitin karkashin jagorancin Justice Adesola Sidik, ta karbi korafe-korafe 26 daga mutane masu zaman kansu da kungiyoyin fararen hula.

Bugu da kari, kwamitin a jihar Kaduna har yanzu ba ta tattara yawan koke-koken da aka karba ba. Sakatariyar kwamitin, Hajiya Hajaratu Abubakar, ta ce, kwamitin ba shi da ikon tantance koke-koken da aka gabatar saboda sakatarorin kananan hukumomin jihar 23 har yanzu ba su gabatar da irin wadannan bayanai ga kwamitin ba.

A jihar Ekiti, Shugaban kwamitin, Mai Shari’a Cornelius Akintayo, ya tabbatar da cewa, kwamitin ta karbi koke-koke 22 daga mambobin jama’a. Kwamitin mai mambobi 12, wanda Gwamna Kayode Fayemi ya kaddamar an ba ta watanni shida don ta sauke aikin da aka ba ta.

A jihar Bauchi, kwamitin mutane 17, wanda Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar, karkashin jagorancin mai shari’a Habibu Idris, sun samu korafi har sau hudu. Kwamitin mai mambobi 10 karkashin jagorancin mai shari’a Babatunde Garba a jihar Kwara, ta karbi korafe-korafe 18 yayin da takwaransa na jihar Filato wanda Gwamna Simon Lalong ya kafa kuma, mai shari’a Justice Philomena Lot, ya karbi korafe-korafe 44.

Kwamitin na jihar Bayelsa, wanda Gwamna Douye Diri ya kaddamar kuma karkashin jagorancin Mai shari’a, Young Ogolata karbi koke-koke 20. Kwamitin da Mai Shari’a Aloy Nwankwo (mai ritaya) ya jagoranta a jihar Ebonyi ta karbi koke sama da 15 daga mambobin jama’a.

Jihar Kano da wasu sauran jihohi biyar har yanzu ba su kafa kwamitocin Shari’ar ba:

Ba kamar sauran jihohi 30 ba, Jihohin Kano, Kebbi, Sokoto, Zamfara, Borno da Yobe har yanzu ba su kafa kwamitocin a jihohinsu ba.

A jihar Kano, har yanzu gwamnatin jihar ta kasa kafa kwamitin shari’a, duk da kiraye-kirayen da masu rajin kare hakkin dan adam a jihar ke yi na a kafa wannan kwamiti don jin korafe-korafe daga mazauna garin da masu rajin kare hakkin dan Adam kan ayyukan SARS a Kano.

Wani mai fafutuka a Kano, Mista Ibrahim Wayya, a karshen makon da ta gabata, ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Ganduje da ya hanzarta kafa kwamitin a jihar don bai wa mazauna yankin damar kai rahoton korafinsu kan rusa rundunar ta SARS.

Duk kokarin da aka yi na tattaunawa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, abin ya ci tura. Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ba ta samu koke koke ba kan cin zarafin da ‘yan sanda ke yiwa jama’a, don ba da sammaci ga kundin tsarin mulkin kwamitin bincike kamar yadda NEC ta umarta.

Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai, Mista Yahaya Sarki, ya fada wa manema labarai cewa, tun lokacin da NEC ta ba da wannan umarnin, gwamnatin jihar ba ta karbi wani koke ba daga mutane ko kungiyoyi ba. Ya ce, “Ba za mu iya kafa kwamitin ba yayin da ba mu karbi wani koke ko korafi ba,” in ji shi.

Jami’an gwamnatin Sokoto da na Zamfara sun ki cewa komai kan batun. Rahoto ya aminta da cewa sun kasance tare da jihar Kebbi kan lamarin. Jihohin Barno da Yobe su ma ba su kafa kwamitin ba, saboda babu wasu bayanai game da cin zarafin ‘yan sanda a kan mutane.

Exit mobile version