An Shigar Da Takardun Lamuni Na Kasar Sin Cikin Tsarin WGBI

Daga CRI Hausa,

A yau Juma’a ne kamfanin FTSE Russell, ya shigar da takardun lamuni na gwamnatin kasar Sin cikin alkaluman asusun kasa da kasa na WGBI, karkashin tsarin FTSE.

Babban bankin kasar Sin ya yi maraba da wannan mataki, wanda ya kara shaida amincewar da masu zuba jari na kasa da kasa suka yi da tsarin kasar Sin, na bunkasuwar tattalin arzikin kasa cikin dogon lokaci, da dorewar ci gaban salon bude kofa ga sauran sassan duniya. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version