An Shirya Bikin Yayata Shawarar Raya Kasa Da Kasa A Hedkwatar MDD
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Shirya Bikin Yayata Shawarar Raya Kasa Da Kasa A Hedkwatar MDD

byCMG Hausa
2 years ago
MDD

A ranar Laraba 19 ga watan nan ne hukumar hadin gwiwa kan raya ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin, da zaunanniyar tawagar wakilan kasar Sin dake MDD, da hukumomin MDD da abin ya shafa, suka shirya bikin yayata manufa cikin hadin gwiwa, mai taken “sabon salon ci gaban shawarar raya kasa da kasa, da sabon matakin ajandar tabbatar da ci gaba mai dorewa”. An gudanar da bikin ne a hedkwatar majalisar dake birnin New York na kasar Amurka.

Shugaban hukumar hadin gwiwa kan ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin Luo Zhaohui, ya gabatar da muhimmin jawabi yayin bikin, inda ya bayyana cewa, muhimman shawarwarin da kasar Sin ta gabatar, kamar su gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, da gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, da raya kasa da kasa, sun gabatar da dabarun kasar Sin a fannin aikin sake farfadowar dukkanin duniya.

  • Bangaren Sin: Ya kamata Al’ummar Kasa Da Kasa Ta Goyi Bayan Kasashen Yankin Manyan Tabkuna Wajen Gina Makomar Bai Daya

Kaza lika makasudin kokarin ingiza zamanintarwa iri ta kasar Sin wanda kasar ke yi, shi ne samun ci gaba mai inganci, da bude kofa ga ketare bisa matsayin koli, kuma duk wadannan sun tattara fasahohi masu daraja, tare kuma da samar da dabaru na hikima da ake iya koya, karkashin muradun tabbatar da dauwamammen ci gaba.

Luo ya jaddada cewa, idan ana fatan aiwatar da shawarar raya kasa da kasa, ya dace a cimma matsaya guda, a hada kai karkashin jagorancin MDD. A sa’i daya kuma, a gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu ci gaba da kasashe masu tasowa.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da bin tunanin gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, domin kafa huldar abokantaka tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a cimma burin raya kasa da kasa baki daya.

Sannan kakakin maaikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kiran da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, game da bukatar kiyaye tsaron duniya ya samu yabo da amincewa daga sassan kasa da kasa a cikin shekara guda, kuma ya zuwa yanzu, kasashe fiye da 80, da wasu kungiyoyin kasa da kasa sun nuna goyon baya ga hakan.

Wang Wenbin ya kara da cewa, Sin ta sa kaimi ga yin shawarwari game da kiyaye tsaro a tsakanin kasa da kasa, da sa kaimi ga kasashen nahiyar, wajen gudanar da taron farko na kiyaye zaman lafiya a tsakanin Sin da kasashen yankin kahon Afirka, inda suka cimma daidaito kan shimfida zaman lafiya, da samun bunkasuwa, da sarrafa harkokin kasa a yankin, tare da tabbatar da tsaron nahiyar Afirka baki daya.

Ban da wannan, kasar Sin ta kuma zaburar da bangarori daban daban, da su yi hadin gwiwa a fannonin yaki da cutar COVID-19, da yaki da taaddanci, da kiyaye halittu, da shaanin yanar gizo, da samar da hatsi, da batun sauyin yanayi da sauransu.

Wang Wenbin ya ce, Sin tana fatan yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen rungumar tunanin kiyaye tsaro bisa tsarin bai daya, da raayoyin bangarori daban daban, da hada kai wajen tinkarar kalubalen tsaro, da sauran matsaloli da ba na tsaro ba, don sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwar bil Adama tare. (Mai fassarawa: Jamila Zhou, Zainab Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Next Post
Nijeriya Ta Sanya Hannu A Yarjejeniyar Amfani Da Fasahar Shuka Itatuwa Da Kasar Netherlands

Nijeriya Ta Sanya Hannu A Yarjejeniyar Amfani Da Fasahar Shuka Itatuwa Da Kasar Netherlands

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version