Connect with us

LABARAI

An Tabbatar Mutum 12 Da Aka Gwada Ba Su Dauke Da Cutar Korona A Jihar Zamfara

Published

on

Binciken da aka gudanar akan wasu al’umma jihar Zamfara 12 don ganin ko suna dauke da cutar korona, gwajin da aka gudanar a hali yanzu ya nuna cewa, bas u dauke da cutar, wannna abiu farin ciki ne ga dukkan al’ummar jihar Zamfara.
‘Godiya ta tabbata ga Allah, sakamakon jita-jitar da ta zagaya gari cewa Bashir Bala wanda aka fi sani da Baban Bola na karamar hukumar kauran Namoda ya sulalo zuwa Zamfara jim kadan bayan halarta da kuma taba makarar marigayi Abba Kyari. Hukumar hana yaduwa da kiyaye dokar KORONA ta Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawallen Maradun bata yi kasa a gwiwa ba wajen kama shi da kuma killace shi kamar yadda hukumar NCDC ta tsara.
Haka zalika sakamakon gwajin da aka yi mashi tare da wasu mutane goma 12 ya fito kuma babu mai dauke da cutar korona a cikin su.
Amma duk da haka za’a cigaba da killace su har sai an tabbatar da suna da cikakkiyar lafiyar da ba za ta zama barazana ga al’umma ba.
Al’umma jihar Zamfara na godiya da kokarin mai daraja Gwamna Matawalle zabin Allah, jagoran zaman lafiya Hon. Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, a bisa matakan da ya dauka na ganin an dakile bazuwar cutar a jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: