Connect with us

NOMA

An Tallafa Wa Manoma Da Buhunan Takin Zamani 100 A Abuja

Published

on

Shugaban karamar Hukumar babban birinin tarayyar Abuja Alhaji Abdullahi Adamu Candido ya kaddamar da raba takin ta hannun kansila mai wakiltar mazabar Wuse Aliyu Mathias wanda ya rarraba taki sama da buhu 100 ga manoman yankin,inda kuma ya yi kira ga wadanda suka samu takin su yi amfani da shi domin samun kyakyawar yabanya a gonakinsu, ya kuma gargade su kan kada su sayar da takin, su tsaya su ba da gudunmawarsu ga shirin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na habaka noma Nijeriya da abinci.

Ya kuma gode wa, Alhaji Abdullahi Candido kan wannan karamci da ya yi wa al’ummar mazabarsa ta Wuse na samar musu da takin zamanin a lokacin da suke bukatarsa, ya kara da cewa, hakika al’ummar mazabar Wuse sun amsa kiran da Shugaba Buhari ya yi na komawa gona, don haka ba da wannan taki, somin tabi ne wajen samar da abubuwan da za su inganta rayuwar al’ummar mazabarsa.
A jawabin Shugaban Jam’iyyar APC na Wuse, Alhajui Salisu Abubakar Baure ya gode wa Alhaji Abdullahi Adamu Candido da Mista Aliyu Mathias domin ba wa al’ummarsu takin, wanda ya ce hakika zai taimaka wajen bunkasa harkar noma a yankin.
Ya kuma shawarci wadanda suka samu takin su yi amfani da shi domin samun ci gaba.
Manoman da suka samu takin sun gode wa kansilan nasu domin wannan kokarin da ya yi musu kuma sun yi alkawarin ba za su ba shi kunya ba da manoma 100 ne suka amfana daga rabon takin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: