‘Yan sandan kasa da kasa sun mayar da Abdulrasheed Maina Nijeriya, bayan an damke shi a Jamhuriyar Nijar a farkon makon nan.
A wani sako da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta wallafa wasu hotuna da ke nuna Maina a filin jirgi yana sauka daga jirgi tare da ‘yan sanda. Tun a daren Litinin ne jami’an sirri na Nijar din suka kama Maina.
Abdulrasheed Maina, wanda tsohon shugaba ne a kwamitin yi wa tsarin fansho na Nijeriya garambawul, na fuskantar tuhuma har guda 12 tare da wani kamfani,hukumar EFCC ce ta gabatar da tuhumar a kansu.
EFCC na zargin Maina da amfani da asusun wani kamfani wajen halatta kudin haram har kusan naira biliyan biyu, wanda cikin kudin ne ake zargin ya sayi wasu kadarori a Abuja.