Zubairu M Lawal" />

An Tsame Ma’aikatan Gwamnati A Rabon Tallafin Abincin Karamar Hukumar Doma  

Shugaban karamar hukumar Doma da ke jihar Nasarawa Alhaji Rabo Sani ya gargadi masu rabon kayan masarufin da gwamnatin jihar ta aiko zuwa karamar hukumar Doma cewa su raba kayan yadda ya dace.

Honorabul Rabo Sani ya gargadi masu aikin rabon da suyi aiki tsakaninsu da Allah bahu batun nuna bambamcin addini ko jam’iyya ko kabila.

Ya ce, wannan kayan abincin gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule sai da ya gargadi masu aikin rabon kayan.

Gwamnan da kanshi yayi kwamitin da zasu raba kwyan a dukkanin kananan hukumomi. Cikin kwamitin akwai Shugabannin kananan hukumomi da Sarakunan gargajiya da Malaman addinai, saboda baya bukatar a samu matsala wajen raba kayan.

Shugaban karamar hukumar ya kara jan kunnesu dasu raba kayan nan ga Talakawa kamar yadda Gwamna Abdullah Sule ya ummurci a raba. Kada a kuskura a baiwa ma’aikacin Gwamnatin ko masu hannu da shuni.

Shima a nasa jawabin daya daga cikin yan kwamitin rabon kayan masarufin Alhaji Yusuf Musa Shugaban kafar yada labarai na gidan Radio da Talabijin na Jihar Nasarawa (NBS).

Ya kara jan hankalin masu rabon da suyi amfani da tsarin da Gwamnan jihar ya ce ayi mazabe mazabe. Sannan suyi amfani da takarda duk wanda ya karbi kayan tallafin zai rubuta sunan shi da lambar waya saboda za a maidawa gwamnati da wannan takardan su zasuyi bincike.

Wannan kayan abincin wanda masu hannu da shuni na Nijeriya suka ba da tallafi ne lokacin hargitsin cutar korona bairus. Da shine gwamnatin kasa ta saya kayan abinci ta raraba zuwa jihohi domin a rabawa Talakawa.

Adadin kayan abincin da ya iso karamar hukumar Doma daga hannun gwamntin jihar Nasarawa.

Buhun Shinkafa 352, Buhun Shuga 403, Buhun Samombita 1,512, Indomi 5,166, Mangyada jarka 40

Karamar hukumar Doma tana da Gunduma 10  da mazabe 126.
Tuni dai aka cigaba da rabon kayayakin a safiyar ranar alhamis 9-7-2020. Karkashin jagorancin Rabo Sani Shugaban karamar hukumar Doma . inda ya wakilta dukkanin kansilolin dake karamar hukumar Doma da su wakilce shi su sanya ido wajen ganin anyi rabon kayan cikin adalci.

Exit mobile version