Umar A Hunkuyi" />

An Tsare Mai Aikin Fenti A Kan Satar Talabijin

Bayan amsa laifin sa na fasa gida da kuma satan Talabijin wanda kimar sa ya kai Naira 35,000, wani lebura mai aikin fenti mai kimanin shekaru 23, Tunde Adeyemi, a ranar Laraba, kotu ta yanke hukunci a kan zai ci gaba da zama a Kurkukun Kiri-kiri.
Otun Majistare ta Ikeja, wacce ta yi wannan hukuncin ta ce, wanda ake karan zai ci gaba da zama ne a gidan Kurkukun har sai an yi hukunci a rana ta gaba da aka daga ta yin hukuncin, watau 15 ga watan Afrilu.
Adeyemi, wanda mazaunin Anguwar Mushin ne ta Legas, ya amsa laifin tuhumomi ukun da ake yi ma shi ne na fasa gida, sata da kuma yunkurin cin amana a gaban mai shari’a, M.O Tanimola.
Tun da farko, Dan sanda mai gabatar da kara, Insifekta Aondohemba Koti, ya shaidawa kotun cewa, wanda ake karan ya aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Afrilu, a Olorunsogo, Mushin, Lagos.
Ya ce, wanda ake karan ya fasa kofar gidan wanda yake karan ne, Mista Oluwatimileyin Gabriel, da nufin yin sata.
“Wanda ake karan ya lalata makullin kofar gidan da kuma kofar wanda yake karan, sannan ya sace ma sa Talabijin din nashi.
Koti ya ce, makwabta ne suka kama wanda ake karan a lokacin da yake fita daga cikin gidan. Alkaliyar kotun ta ajiye ranar 15 ga watan Afrilu, domin ci gaba da shari’ar.

Exit mobile version