An Tsaurara Matakan Tsaro A Hedikwatar Hukumar INEC Ta Jihar Kano

An tsaurara matakan tsaro a babban ofishin hukumar zabe na jihar Kano, wannan ya biyo bayan dakatar da karbar sakamakon zaben gwamna da ake jira daga karamar hukumar Nasarawa, saboda barazanar tsaro da ake fuskanta wajen kawo sakamakon zaben, sannan an jibge wasu jami’an tsaron a hanyar zuwa sansanin mahajjata na jihar Kano.

Dadin dadawa an takaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa a zagayen ofishin hukumar zaben, inda jami’an tsaro, jami’an hukumar zabe da ‘yan jaridu kawai ake bari suke kai kawo a zagayen hukumar zaben, duk babu mata matsalar tsaro a cikin garin Kano, inda jama’a suke gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

Duk an bude wasu bankuna da manyan kantinan siye da sayarwa, amma ba a bude kasuwowin Sabon Gari da na Rimi ba, wasu masu rumfuna a kasuwar Sabon Gari sun ce ba za a bude kasuwar ba, har sai hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Kanon da ake ta dako, saboda gudun faruwar irin abubuwan da suka faru a baya.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jinkirta karbar sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa ne saboda barazana tsaro da ake fuskanta, amma da zarar yanayin ya yi kyau za a karbi sakamakon wanda shine na karshe, daga shi za a bayyana sakamakon zaben.

Exit mobile version