Umar A Hunkuyi" />

An Tsawaita Wa’adin Mukaddashin Alkalin-Alkalai Na Kasa Da Watanni Uku

Hukumar shari’a ta kasa ta tsawaita wa’adin nadin da aka yi wa mukaddashin Alkalin-Alkalai na kasa, Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, da wasu watanni uku a nan gaba.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta bakin Kakakin ta, Soji Oye, cewa ya yi, shawarar tsawaita nadin da aka yi wa mukaddashin Alkalin-Alkalan an yi ta ne a taro na 88 na hukumar da aka yi a ranar Alhamis.
Ya kara da cewa, an yi hakan a bisa bukatar neman yin hakan da shugaba Buhari ya yi.
Sanarwar na cewa, “Hankalin hukumar shari’a ta kasa ya kai ga wani rahoto da wata kafar yada labarai ta yanar gizo da kuma wata jarida mai fita a kullum-kullum suka wallafa, inda suke bayanin cewa, a mako mai zuwa ne hukumar shari’a ta kasa a ta yi zama domin ta tsawaita wa’adin aikin mukaddashin Alkalin-Alkalai na kasa, Mai Shari’a Dakta I.T. Muhammad, a matsayin Alkalin-Alkalai na kasa.
“A sabanin wannan rahoton na su, tabbas hukumar shari’a ta kasa ta yi zamanta a ranar Alhamis, 18 ga watan Afilu, 2019, zamanta na 88, inda ta duba takardar da shugaba Buhari ya aiko mata da shin a neman tsawaita wa’adin nadin mukaddashin Alkalin-Alkalan, Mai Shari’a I. T. Muhammad, CFR, a matsayin mukaddashin Alkalin-Alkalai na kasa, da wasu watanni uku a nan gaba, tuni ma hukumar ta aikewa da shugaban kasa hakan domin neman aminewar shi. Harin Bama-Bamai A Kasar Sri Lanka Ya Hada Da Mutanan Amurka, Ingila Da Sauran Su
Hukumomi a kasar Sri Lanka, sun bayyana cewa, akalla mutanan kasashen waje 35 ne da suka hada da ‘yan kasar Amurka, Ingila da sauran su suka mutu a hare-haren bama-bamai biyu da aka kai a babban birnin kasar, Colombo, a ranar Lahadi, lokacin da ake addu’o’i da shagulgulan bikin Ester.
‘Yan sanda a kasar sun ce ya zuwa yanzun ana da tabbacin mutuwar mutane 137 zuwa 156.
Harin wanda yake shiryayye ne, an kai shi ne da misalin karfe 8:45, na safiyar Lahadi.
Babban daraktan Lafiya na kasar, Janar Anil Jasinghe, ya tabbatar da hakan.
Akalla har sau shida ne aka shaidi wasu abubuwa suna ta fashewa. Manyan Cocina uku a biranan Colombo, Negombo da Batticaloa ne aka hara a lokacin na bikin Ester.
Kimanin mutane 400 ne suka jikkata, a yanzun haka suna karban magani a babban Asibitin birnin na Colombo.
Kwanaki 10 da suka wuce, shugaban hukumar ‘yan sandan kasar ya yi gargadi da yiwuwar kai harin bam din, kafin tashin bama-baman a ranar Lahadi, wanda wasu ‘yan kunar bakin wake suka shirya kaiwa wasu fitattun Cocina a kasar,” kamar yanda gargadin na ‘yan sanda ya suna.
“Wata majiya ta sirri daga wajen kasar ta labarata cewa, kungiyar NTJ (National Thowheeth Jama’ath) tana yin wani shiri na kai harin kunar bakin waken a wasu fitattun Cocina da kuma ofishin jakadancin kasar Indiya da ke birnin na Colombo,” in ji sanarwar gargadin.
NTJ, kungiya ce ta Musulmi masu tsattsauran ra’ayi a kasar ta Sri Lanka, wacce lamarin ta ya fito fili a shekarar da ta gabata inda aka alakanta ta da lalata gunkin masu bin Addinin Buda a kasar.
Firaministan kasar ta Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya yi tir da kai hare-haren da suka kashe akalla mutane 137 a ranar ta Lahadi, ya siffanta harin da cewa aiki ne na wawaye, sannan ya ce gwamnati tana yin duk abin da ya dace na ganin ta shawo kan lamarin.

Exit mobile version