Daga Khalid Idris Doya
Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta tsige Kakakinta Abubakar Sadiq Kurba a yau din nan.
‘Yan majalisu 16 daga cikin 24 na majalisar dokokin jihar ne suka rattaba kuri’ar tsige shi nan take.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar Shuaibu Adamu shi ne ya sanar da jerin sunayen ‘yan majalisa 16 da suka nuna rashin gamsuwarsu da salon jagorancin Kakakin inda suka amince da tsige shi, kudurin wanda Saddam Bello, mai wakiltar mazabar Funakaye ya gabatar.
Bayan shi ma, shugaban masu rinjaye na majalisar Samuel Markus shi ma an tubeshi kan wannan mukamin nasa wanda nan take Hon. Yahaya Kaka ya sauya shi.
Cikakken labarin na tafe.