An Tsige Kakakin Majalisar Jihar Filato

Daga Sulaiman Ibrahim,

An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Hon Abok Ayuba Nuhu.

An maye gurbinsa da Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana ta karamar hukumar Bassa ta jihar.

Mambobi 16 daga cikin 24 na majalisar ne suka kada kuri’ar amincewa da tsige shi a zauren majalisar a ranar Alhamis.

An ruwaito cewa an akwai rashin jituwa tsakanin Gwamna Simon Lalong da shugaban majalisar tun bayan harin da aka kai a unguwar Yelwan Zagam da ke yankin Jos ta Arewa, inda aka kashe mutane da dama.

Bayan harin, kakakin majalisar ya fara sukar gwamnan a fili.

Ya kuma daina halartar ayyukan gwamnati a jihar.

Exit mobile version