Connect with us

LABARAI

An Tsinci Gawa 23 A Dajin Zamfara

Published

on

An tsinto gawarwakin mutane 23 a cikin dajin karamar hukumar Zurmi, ta Jihar Zamfara, a ranar Juma’a da yamma.
Gawarwakin, wasunsu harbin bindiga ne a jikkunansu sa’ilin da kuma wasunsu an yi masu yankan rago ne.
Hakan dai ya jefa tsoro a zukatan al’ummun da ke kewayen, lamarin dai ya faru ne ‘yan watanni kadan da wasu mahara da ke dauke da makamai suka kashe gomomin mutane a yankin, wurin yana da nisan kimanin kilomita 100 ne daga babban birnin Jihar Gusau.
A watan Fabrairu, an kashe mutane 41 lokacin da wasu da ake kyautata zaton barayin shanu ne suka kai farmaki da bindigogi, a wata kasuwa da ke kauyan Birane, ta karamar hukumar Zurmi.
Wakilinmu ya jiwo cewa, mutanan yankin ba su iya gane ko mutum guda ba daga cikin mutanan da aka kashe, wanda hakan ke nu na cewa, watakila mutanan ba daga yankin ne suka fito ba. Al’umman yankin suna tunanin watakila mutanan sun taka sawun barawo ne, don kuwa ga alamu sun yiwo hijira ne daga wani wajen a kan hanyarsu ta wucewa zuwa wani wurin na daban sai lamarin ya rutsa da su. Tuni dai sun ce sun yi jana’izar mamatan.
Rundunar ‘yan sandan Jihar ta Zamfara ta ce ta fara binciken dalilin faruwan lamarin.
Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu, ya ce, ‘yan sanda sun sami labarin tsintar gawarwakin da aka yi cikin daji a karamar hukumar ta Zurmi.
Sai dai wani mazaunin kauyan Boko, wanda ke kusa da wajen da lamarin ya auku, ya shaida wa wakilinmu cewa, “’Yan Bangan sa Kai,” ne suka kashe mutanan.
“Wannan dajin wata mafaka ce ta masu aikata laifuka, shi ya sanya a lokacin da ‘yan bangan suka ga mutanan sai kawai suka hau su da kisa,” in ji majiyar tamu wacce ba ta so a ambata sunanta ba. “Ba mu san tahakikanin inda mutanan suka fito ba, ba mu kuma san ainihin inda za su ba,” in ji majiyar tamu.
“A kwanan nan ne aka sace wasu shanu guda 10, shi ya sanya ‘yan bangan suka bazama domin kare al’umman yankin daga munanan hare-haren na barayin shanu.
A cikin ‘yan shekarun nan an yi asarar daruruwan rayuka da dukiyoyin bilyoyin naira daga ayyukan ta’addancin barayin shanun a Jihar. Hare-haren ne kuma suka tilasta wa da yawa daga mazauna yankin barin gidajensu zuwa yin kaura a makwabciyar Jihar, watau Jihar Katsina.
A makon da ya shige ne, Gwamna Abdul’aziz Yari, ya ce zai ajiye mukaminsa na babban mai kula da harkar tsaro na Jihar, saboda mukamin bai ba shi ikon bayar da umurni ga hukumomin tsaron da ke aiki a cikin Jihar ba.
“Muna fama da matsalar tsaro matuka a cikin shekarun nan, amma duk da ina mukamin gwamna, kuma babban kwamandan tsaro a Jihar nan, ba zan iya bayar da umurni ga jami’an tsaron ba.
Ya ce, Jihar ta dulmiya bilyoyin Naira domin taimaka wa hukumomin tsaro, domin su kawo karshen wannan mummunar barnar da ake yi mana, amma sam hakan bai samu ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: