Yusuf Shuaibu" />

An Tsinci Gawar Wata Mata Tsirara Kusa Da Makarantar Firamare

An tsinci gawar wata mata tsirara wacce ake zargin an yi mata fyade a kusa da makarantar firamare ta United Primary School da ke Oba cikin karamar hukumar Idemili ta kudu ta Jihar Anambra.

Kakakin rundunar jami’an tsaro masu tsaron fararen huda (NSCDC), Mista Edwin Okadigbo ya bayyana cewa, mutanen yankin ne suka tsinci gawar matar a ranar Talata da safe, sannan suka sanar wa rundunarsa da ke yankin. Ya kara da cewa, an tsinci gawar matar ne tsirara wanda ake zargin an mata fyade kafin ta mutu. Ya ce, “a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2020 da misalin karfe 7.30 na safe ne, a kusa da makarantar firamare na United Primary School da ke Oba cikin karamar hukumar Idemili ta kudu, aka tsinci gawar wata mata tsirara wacce ake zargin an yi mata fyade ne. “Shugaban hukumar NSCDC reshen karamar hukumar Idemili ta kudu, SC Ochie Paul tare da jami’ansa suka ziyarci wajen da lamarin ya faru, inda suka ga gawar matar, nan take suka dauke gawar domin kar ta zama cuta ga yaran makaranta.”

Okadigbo ya ci gaba da cewa, an dauki hoton gawar matar sannan an sanar wa sauran jami’an da masarautar Igwe da kuma shugaban karamar hukuma. Ya ce, a halin yanzu ana gudanar da bincike a kan musabbabin mutuwar matar tare da gone ‘yan’uwanta.

Exit mobile version