An Tura Karin Dakaru A Zamfara Yayin Da Wa'adin Harajin Turji Na Miliyan 30 Ya Cika
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Tura Karin Dakaru A Zamfara Yayin Da Wa’adin Harajin Turji Na Miliyan 30 Ya Cika

bySulaiman
1 year ago
Zamfara
An tura karin sojoji a garin Moriki da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, yayin da wa’adin biyan harajin  Naira miliyan 30 da Kasurgumin shugaban ‘yan bindigan nan, Bello Turji ya kakaba wa al’umma, ya cika.
Turji ya saka harajin Miliyan 30 a kan al’ummar yankin biyo bayan kashe masa shanu sama da 100 da sojoji suka yi masa kimanin makonni uku da suka gabata.
  • Kasar Sin Za Ta Zurfafa Hadin Gwiwa Da Sauran Kasashe A Bangaren Tsaron Intanet
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Al’ummar Borno Kan Ambaliyar Ruwa
An rahoto cewa, sojoji sun harbe shanun ne a Dumfawa, wani kauye tsakanin Moriki da garin Shinkafi a cikin watan Agusta.
Da yake tabbatar da tura sojojin, wani mazaunin yankin, Aminu Musa, ya ce, an tura karin sojoji yankin a kwanakin baya.
“Baya ga sojoji, gwamnatin jihar ta kuma aike da karin jami’an tsaronta, na CPG zuwa yankin domin karawa jami’an kaimi.
“Mun yi farin cikin ganin jami’an tsaro a cikin yankunan mu. Shugaban rundunar ya ba mu tabbacin kare rayukan mu.”
Wani mazaunin garin, Iliyasu Ali, ya ce duk da karin jami’an tsaro da aka tura, akwai damuwa a tsakanin mazauna garin”.
“Akwai firgici da damuwa a tsakanin mazauna garin. Waɗannan ‘yan bindigar ba su da tausayi. Za su iya kai farmaki ga al’umma. Suna ɗauke da muggan makamai fiye da na sojoji. Don haka, jama’ar mu sun shiga cikin firgici matuka ganin cewa yau wa’adin biyan harajin ya kare.
“Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru daga yau zuwa nan gaba. Tabbas ba mu biya harajin ba amma Turji ya yi alkawarin kawar da wannan al’umma idan har muka kasa biyan diyya ga shanunsa da aka kashe,” inji shi.
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Birnin Baoji Na Lardin Shaanxi Da Birnin Tianshui Na Lardin Gansu

Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Birnin Baoji Na Lardin Shaanxi Da Birnin Tianshui Na Lardin Gansu

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version