CRI Hausa" />

An Wallafa Littafi Cikin Harsuna Daban-Daban Kan Jawabin Shugaba Xi Jinping A Wajen Taron Cikar JKS Shekaru 100

Kwanan nan ne madaba’ar tattara bayanai da fassara ta kasar Sin, ta wallafa littafi kan jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a wajen taron cikar jam’iyyar Kwaminis ta kasar shekaru 100 da kafuwa cikin wasu harsuna shida, ciki har da Rashanci, da Faransanci, da Sifaniyanci, da Larabaci, da Japananci da kuma Jamusanci.

Jawabin ya waiwayi wasu manyan ayyukan da jam’iyyar Kwaminis din ta yi, da dimbin nasarorin da ta samu tun kafuwarta har zuwa yanzu. Haka kuma a cikin jawabin, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasar Sin ta samu nasarar cimma burin gina al’umma mai matsakaiciyar wadata, da bayyanawa duniya babbar niyyar kasar, ta ci gaba da tsayawa, gami da raya tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar a sabon zamanin da muke ciki, da kara kokarin cimma burin raya kasar Sin irin ta zamani, kuma mai karfi, da bin tsarin gurguzu daga dukkan fannoni.
Wallafa littafi kan wannan muhimmin jawabin, zai taimaka sosai ga masu karatu na gida da na waje, don su kara fahimtar yadda jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, take hade kan al’ummun kasar, wajen samun manyan nasarori, da kirkiro sabbin hanyoyin zamanantar da harkoki da sauransu. (Murtala Zhang)

Exit mobile version