Connect with us

ADON GARI

An Wuce Zamanin Da Mace Za Ta Dage Wai Sai Ta Mallake Miji– Zulaihat Yakubu

Published

on

Malama Zulaihat Yakubu Abduljalil, mace mai hazaka, ta ja hankalin ‘yan uwanta matan aure da wadanda ba na aure ba, kan su mike tsaye wajen neman na kansu ka da su zauna jiran wasu su basu. Haka nan ta fada musu dabarar da za su yi maimakon dagewa wajen ganin an mallake miji ko ta halin kaka. Ga dai yadda hirarmu da ita ta kasance:

Assalamu Alaikum, da farko dai masu karatu za su so sanin sunanki da takaitaccen tarihinki
Sunana Zulaiha Yakubu Abduljalil, amma an fi sani na da Oum Banaat, an haife ni a Zaria na yi karatuna duka na Addini da na boko a Zaria, kuma ina da aure da ‘ya’ya hudu namiji daya mata uku.

Yanzu a bangaren aiki ko karatu, sana’a wane mataki kike ko zaman gida kawai kike?
Sana’a na ke yi, sana’o’in nawa kashi kashi ne, ni marubuciya ce ta rubutun Zube ko nace Adabin kasuwar kano. Sannan ina sana’ar yin abinci na Girke-Girke da ya shafi sha’anin musamman na abincin biki ko suna da sauran taruka haka, sannan ina harhada kayan shafe -shafe na ‘Organic’ gyaran jiki da gyaran gashi, kuma ina sana’ar Atamfofi, Leshi, Zannuwan Gado da duk abin da ya zo hannu dai wanda za’a iya juya kwabo ya dawo Naira.

Yanzu kamar mutum yana son fara daya daga cikin wadannan sana’o’i kawai zai fara ne kokuwa akwai shawarwari da za ki iya ba wa mutum?
Fadawa sana’a kai tsaye ba ya yiwuwa, a kalla sai mutum yana da Ilimi ko yaya ne na abin da yake so ya fara, ilimin shi ne zai zama kamar fitila a wajensa matukar yana so ya kai ga gaci , sosai akwai shawarwari da zan iya ba masu sha’awar irin sana’a ta.

Na ji kin ce kina hada kayan shafe-shafe, masu karatu za su jin shin kina koyarwa ne?
To ya zuwa yanzu dai ban fara samun masu koyo ba, amma kofata a bude take ga masu sha’awar koyo.

Masha Allah! Shin ko akwai kalubale da kike fuskanta ko kika taba fuskanta wurin koyon wannan sana’a?
Dukkan al’amura ba a raba su da kalubale a rayuwa, musamman abin da ya shafi sana’a. Zan iya cewa babban kalubale na da na samu a farko ba ga wajen koyon sana’ar bane, saboda na saka son abin a raina ina kiyaye kaidojin koyon dai-dai gwargwado. kalubalen da na samu, na same shi ne, bayan na gama koyo, a lokacin da na fara tallata kayana wato matsalar masu karbar bashi wanda za su karbi kaya su ki biya ko su jinkirta biyan har ya zuwa wani dogon lokaci kafin su biya.

Shin wane irin abin farin ciki ne ko akasinsa da faru dake wanda ba za ki taba mantawa da shi a rayuwarki ba?
Abin da ba zan taba mantawa da shi a rayuwata ba shi ne mutuwar Iyayena, su duka biyun Alhaji Yakubu Abduljalil Sarkin Ruwan Zazzau, da mahaifiyata Hajiya Rahila Yakubu Shafiu. Sai kuma rasuwar ‘yar ‘uwata shakikiyata wacce ta maye gurbin uwa a wajena bayan na rasa mahaifiyata, Haj Rabiatu Yakubu Ita ma ba zan manta Rashin ta ba.

Wacce shawara za ki ba wa mutane game da sha’anin rayuwa ta yau da kullum Wanda idan suka yi koyi ko amfani da ita rayuwa za ta inganta?
Shawara ta ita ce, mu kasance masu rikon gaskiya da hakuri a dukkan yadda rayuwa ta zo mana, sannan mu zama masu riko da sanao’i’n hannu musamman a irin wannan zamani da muke ciki mai wahala mu rage yawan dogaro da jiran sai mun samu aikin Ofis ko da za mu yi aikin gwamnati to ya zamana muna da wata sana’a da muke yi a gefe wanda za ta rika kawo mana kudaden shiga a ko da yaushe kafin shigowar Albashi.

Ko kina ganin akwai wata hanya da gwamnati za ta iya shigowa cikin irin wannan sana’a taku don ba da gudunmawa ko taimako?
Sosai kuwa, hanyoyin daga ciki muna bukatar tallafi na kudade wanda za mu fadada sana’ar tamu da kuma bayar da horo don karin ilimi a kan sana’ar, ta yadda za mu kara inganta kayayyakin da muke yi kasuwar ta zama mai fadi sosai ta yadda har za mu iya daukar wasu ma’aikata da suma za su iya samun abin dogaro da kai a karkashin sana’ar.

Za mu so ki yi wa masu karatu karin bayani kan wannan sana’a taki, saboda kin ambato abubuwa da dama.
Kamar yadda na ambata ni marubuciya ce na fara da sana’ar rubutu inda na rubuta littattafai da dama, sai dai uku ne kadai suka samu shiga kasuwa, kafin na fara girke-girke na abinci da kayan toye-toye da nake yi watau na ‘OUM BANAAT KITCHEN’ wanda ni ce ‘CEO’ kuma ‘FOUNDER’ wanda da shi ne nake daukar dawainiyar ci da sha na duk wani nau’in taro ne na biki ko suna ko taron siyasa da sauran taruka, muna yin abinci da abin sha dai-dai da aljihun mutane a kan farashi mai sauki, kuma a samu biyan bukata haka nan na fadada bangaren da na fara samar da garin tuwo, tsakin fate-fate da na Dambu, garin danwake, garin yaji ina ‘Packaging’ din su, kuma Alhamdulillah suna shiga sosai. Sannan akwai bangaren kayan shafe-shafe da gyaran jiki na ‘OUM BANAAT ORGANICS’, shi kuma ya shafi nau’ikan mayukan gyaran jiki ne gaba daya tun daga gyaran gashi, gyaran fuska da gyaran fata gaba daya sai bangaren kayan kamshi turarukan wuta na hayaki, turaren ruwa na feshi, da su turarukan jiki, haka sai atamfofi da lesuka, zannuwan gado, kamar yadda na ambata.

Wace irin gudunmawa kike da ita da za ki iya ba wa al’umma da za su amfana?
Ina da buri mai yawa a kan sana’ata wacce da ita nake fatan ba da gudunmawata wato fadada sana’ar tawa ta yadda zan taimaki wasu su ma da ke kasana su mike su tsaya da kafafunsu a gaba ina fatan na kai matakin da zan bude wata cibiya da za ta zama tamkar makaranta da za a rika daukan dalibai ana horas da su su ma su samu abin yin domin dogaro da kansu musamman ‘yan uwana mata da ke gidajen aure da suke zaune haka nan babu wata ‘yar sana’ar hannu da suke yi, tare da matasa masu kananan shekaru da suke zaune haka nan ba su ci gaba da karatu ba, kuma babu wata kwakkwarar sana’a da suke yi domin su dogaro da ita, ina da yakinin hakan zai taimaka kwarai, kuma zai amfanar da Alummata insha Allahu .

Wace shawara za ki ba wa mata ‘yan uwanki musamman a bangarena rayuwar aure duba ga zamanin da muke ciki?
Shawarar da zan ba da ita ce, mata su san inda yake masu ciwo su sani an wuce zamanin da mata suke zaune kawai suna jira komai sai miji ya kawo ya basu haka an wuce zamanin da mace za ta daddage ta ce sai ta mallake mijinta ne kadai za su zauna lafiya. Tabbas daga cikin zamowarki cikakkiyar mace kuma Uwa akwai zamo wa mai hakuri da kawar da kai da kula da tsaftar iyali da iya girki tare da ladabi da biyayya sannan Sana’a, matukar ba ki da abin yi a wannan zamani ki sani dukkan wadancan abubuwa da na lissafa su kan zama masu rauni a da yawa-yawan gidajen aure, saboda haka ina mai baku shawara ku tashi ku nemi sana’a mata macen da ke da abin yi kimarta daban ne a idon mijinta da sauran mutane gaba daya, kuma ka da mu raina sana’a komai kankantar ta babu wani kaskantacce a sana’a matukar ba sana’a ce da za ta shafi mutuncin ki ba ki jure ki yi ta za ki samu rufin asiri daidai gwargwado.

Wace shawara za ki bayar don yin tarbiyya ga yara a matsayinki na uwa?
Lamari na tarbiyya a wannan zamani abu ne mai matukar wahala, dole sai mun fara da gyaran namu tarbiyyar mu iyaye idan muna so mu ga daidai a gidajenmu, mu kiyaye iyakokin Ubangiji sai mu yi biyayya ga Allah sai ya duba mana su, haka kuma mu dinga hadawa da addu’a da jan yaranmu a jiki da yi masu nasiha cikin hikima da azanci, haka nan mu kiyaye da kula da su wane ne yaranmu ke mu’amala mu raba su da batagarin abokai, saboda shi tarbiyya naso take yi ko mun basu tarbiyya mai kyau matukar suna cudanya da yaran da ba su da cikakkiyar tarbiyya to za ya zama tamkar muna gini ne da tubalin toka. Haka nan mu kiyaye da yawan hantarar yaro ko zagi ko duka hakan baya shirya yaro se dai ya sa ya kangare zuciyarsa ta yi tauri a yi ta jan su a jiki ana nuna masu kuskuren su a hankali sai su gyara.

Duba da yanayin kasuwancinki ga kuma yara, ta yaya kike iya tafiyar da wadannan ayyuka har da na gida?
Kula da iyali da kuma Sana’a a lokaci daya ba abu ne mai sauki ba gaskiya, amma idan ya zamana akwai fahimtar juna tsakanin abokanan zama abubuwa su kan zamo da sauki. A bangarena ina tsara Lokacina, akwai lokutan iyalina da kuma lokacin aikin sana’ata, musamman da ya zamana na fi Tallata kayana a yanar gizo to zan iya cewa ina da cikakken lokacin kula da iyalina. Domin idan na tura kaya na kan bar lambar tuntuba da adireshi na wanda yana saukaka min haduwa da abokan kasuwancina matuka.
Ko akwai abin da kike son fada ko shawara wacce bamu tambaye ki ba kike son fada?
Abin da nake son fada ita ce godiya da Jinjina ga wannan gidan jarida mai albarka da ta ke ba wa mata dama irin wannan musamman matan da ba a san da su ba masu bai wa ta sana’o’i iri daban-daban wanda wannan jarida ke ba su dama ta fito da su duniya ta gansu. Hakika wannan babban abin a yaba ne, kuma aiki ne mai kyau wanda ina da yakinin zai kara zaburar da mata ‘yan uwana akan kara sanin muhimmancin Dogaro da kan su, ina godiya matuka da irin wannan dama da kuka bani.
Masha Allah, mun gode da yabo, Allah Ubangiji ya huta gajiya Ameen.
Ameen ni ma na gode
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: